Sharrin dake kunshe da fina finan Tarihin Musulunci

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh

Bismillahir-Rahmanir-Raheem.

A yau zan ja hankalinmu ne kan wata musiba da take yawo acikin mu, wannan musiba kuwa itace fina finan tarihin musulunci.

Karantar tarihi abu ne mai matuƙar amfani ga kowata Al’ummah, domin akwai abubuwa da yawa wadda zamu amfana dasu, zamu amfana da hanyoyin da magabatanmu sukayi amfani dashi wurin samun Nasara, da kuma gwagwarmaya da sukayi wurin kafa wannan Addini, hakanan zamu amfana da kurakurai da sukayi domin muma mu kauce mata.

Sabida haka ne Maluman Musulunci sukayi rubuce rubuce masu yawa kan tarihi, suka fara tun daga zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama har zuwa yau basu daina ba, duk abinda ya faru suna rubuta shi domin na baya suzo su karanta su amfana.

Sai dai a wannan zamani namu abin yana canza salo, ta yadda a da rubuta wa akeyi, amma a yanzu sai aka mai dashi fina finai, ta yadda Za’a rinƙa nuna abubuwan tarihin kamar kana ganinsu, duk da cewa wannan hanyar tafi tasiri da tabbatuwa acikin zuƙatan mutane sai dai kuma wannan hanyan na ƙunshe da matsaloli masu yawa.

Wannan matsalolin kuwa sune kamar haka:

A duk lokacin da kaga wani Film na tarihi wanda misali akwai wani sahabi aciki, tofa a duk lokacin da kaji ankira sunan wannan sahabin nan toh wannan hoton Mutumin da ka gani a Film shine zai zo maka a ƙwaƙwalwarka, babban Misali akan haka shine kan Film na yaƙin Badr wanda ya shahara sosai acikin Musulmai, a duk lokacin da aka sanya shi zaka ji Yara sunace ga Bilal. Ga wane ga wane. Toh irin wannan hotunan ne zasu zauna acikin zuƙatansu na wa’innan Sahabbai Allah ya ƙara musu yarda, wanda wannan yana da mummunan tasiri, domin su wa’innan mutane zaka samu dama ƴan Drama ne, toh can zaka sake ganinsu sun fito a wani Film kuma da wata siffa mummuna, suna aikata wasu abubuwa munana a ciki. Wanda wannan zaisa yara su rinƙa ganin kaman wannan Sahabin ne a haƙiƙa.

Ni ya faru dani: farkon Fitowar Film na Umar wanda ya shahara sosai, na fara kallonsa, kuma na fara jin daɗinsa sosai, amma daga baya sai na fara fahimtar wannan mummunan tasiri na wannan Film ɗin a ƙwaƙwalwa ta, ta yadda duk lokacin da naji Sunan Umar Allah ya ƙara masa yarda a karatu sai hoton wannan Mutumin da na kalla a film ɗin ya rinƙa zuwa min, nayi nayi na cire shi a ƙwaƙwalwa ta amma abin yaci tira. Sai dai kawai na kau da kai da hankali na zuwa wani tunani na daban Amma wannan hoton bazai gushe ba. To wannan a matsayi na na babba kenan ina kuma ga yaro ƙarami?

Sannan yana daga cikin Matsaloli da wa’innan fina finai suka ƙunsa: rashin ingancin wasu daga cikin abinda ake nuna wa, wasu riwayar zaka ga basu inganta ba, amma duk da haka zaka ga suna kawosu basu tantancewa kamar yadda duk wanda ya kalli Film na yaƙin Badr kuma ya karanta shi a littafai ingatattu zai fahimci haka.

Wannan kaɗan kenan daga cikin wa’innan matsaloli wanda mafi girmansa shine wanda na ambata a sama.

Ya zama dole ga iyaye su kiyaye nuna wa ƴaƴayensu irin wa’innan fina finan hakanan suma su ƙaurace wa kallon irin wa’innan fina finan, su nemi wata hanya ta daban wurin karantar tarihi, kaman littafi ko sauti.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories