Zunubi mai gudana bayan mai shi ya mutu

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi bayani a hadisi wanda Muslim ya rawaito hadisi mai lamba 1631 cewa idan ɗan Adam ya mutu ayyukansa duk sun tsaya sai abubuwa guda uku:

  • Sadaqa mai gudana: kamar mutum ya haƙa rijiya ya bari mutane su rinƙa amfani dashi kodai wani abu makamancin haka.
  • Ilimi wanda za’a rinƙa amfana dashi: mutum ya karantar da Al’ummah su cigaba da amfana da wannan ilimi har bayan ransa
  • Ɗa na gari wanda yake masa addu’a: mutum ya mutu ya bar ɗa na gari ya rinƙa yi masa addu’a bayan bashi nan.

Wa’innan sune abubuwa uku da mutum zaici gaba da amfana dasu bayan mutuwarsa.

Toh bayan wannan akwai kuma Zunubi mai gudana wanda mai shi zai aikata ya mutu zunubi ya cigaba da samunsa a ƙabarinsa, Musamman a wannan zamani na wayar hanu wanda zakaga mutane suna yaɗa alfasha. Toh ka sani ya kai mai yaɗa irin wannan alfasha duk yaɗa wa da kayi sau ɗaya kana da zunubi, haka nan wanda ka tura masa shima yaje ya tura wa wani toh kana da wani zunubi. Haka nan in mutane dubu ne wannan Alfasha ya isa zuwa garesu a ta dalilin ka toh kana da zunubin ko wanne daga cikinsu. Domin kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya bada labari ne a hadisi da Muslim ya ruwaito hadisi mai lamba 2674 Annabi yace:

Wanda yayi kira zuwa ga shiriya yana da kwatankwacin ladan wa’inda suka bishi ba za’a rage musu komai na ladansu ba, haka nan wanda yayi kira zuwa ga wani ɓata yana da zunubi kwatankwacin zunubin wa’inda suka bishi kan wannan ɓata ba za’a rage musu komai daga zunubinsu ba.

Yana daga cikin ƙira zuwa ga ɓata yaɗa Alfasha tsaƙanin Musulmai, domin hakan zai iya saka wani yaje ya aikata wannan alfashan. Hakanan yana daga cikin ƙira zuwa ga ɓata ƙirƙirar wani bid’ah.

Allah yana cewa acikin Suratu Nur aya ta 19:

Lalle ne wa’inda ke son Alfasha ta watsu cikin wa’inda sukayi Imani suna da azaba mai raɗaɗi anan duniya da kuma lahira.

Ya kamata Musulmi ya kula duk abinda zai tura a wayarsa ko kuma zai kira mutane su aikata shi ya tabbata abu ne mai kyau sabida kada wannan narko na azaba ya riske shi.

Sannan mu sani cewa masu yaɗa wa’innan alfasha cikin Musulmi in basu tuba ba har suka mutu toh Suna da azaba mai raɗaɗi kuma a kullum suna ƙara samun zunubi ne da adadin wanda wannan alfasha da suka yaɗa ya riska, kuma babu wanda yasan shekaru nawa za’ayi kafin ayi tashin Al-Qiyama.

Toh sai mutum ya tuna yanzu ka tura wani batsa wa mutane. Wannan batsa ya cigaba da yaɗuwa shekaru aru aru kullum kana samun zunubi, shin kayi tanadin aiki na gari da zai share wannan zunubin? Musamman a irin wannan zamani na yanar gizo, wanda da zarar ka tura abu kafin mintoci kaɗan ya zagaye duniya. Ya kamata mu lura mu kula sosai kafin mu yaɗa duk wani abu.

Allah yasa mudace. Ya bamu ikon tuba zuwa ga Allah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories