Hadith: Ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Abdullahi Bin Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya Rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar. Samartakan ka kafin tsufan ka, lafiyar ka kafin rashin lafiyar ka, wadatar ka kafin talaucin ka, sararin ka kafin shagaltuwar ka, rayuwar ka kafin mutuwar ka

Sahihut-Targhib Sheikh Albani: 3355

A wannan hadisi Annabi yana koya mana yadda zamu ribaci rayuwar mu baki ɗaya.

Muyi amfani da samartakan mu kafin tsufar mu: domin lokacin samartaka ne mutum yake da cikakken ƙarfin, duk abinda yake so yayi a lokacin zai fi samun daman yi, amma da zarar mutum ya tsufa to wani abin dole ya gagare shi,

Muyi amfani da lafiyar mu kafin Rashin lafiyar mu: shi rayuwa mutum bazai dawwama da lafiyar sa ba a kowani lokaci, dole wani lokaci rashin lafiya zai kama mutum, wani lokaci ma da zarar rashin lafiyar ta kama mutum to shikenan har ya mutu ba zai samu sauƙi ba, shiyasa anan Annabi yake umartan mu da muyi amfani da lafiyar mu kafin rashin lafiya ta riskemu abinda mukeso muyi mu kasa yi saboda rashin lafiya.

Muyi amfani da wadatar mu kafin talauci: Shi arziƙi bashi da tabbas, zai yiwu yau kana dashi gobe kuma ka wayi gari babu, saboda haka kayi amfani da damar ka, lokacin da kake dashi kayi amfani dashi ta hanyar da ta dace, wurin taimaka wa Addini da ayyukan alheri. Idan aka jarrabe ka da babu to ka riga kayi a baya.

Muyi amfani da Rarar lokaci da muke dashi kafin abubuwa suyi mana yawa: a duk lokacin da ka samu dama da sarari to kayi amfani dashi kafin wani abu yazo ya shagaltar da kai, kayi amfani da lokutan ka wurin neman ilimi da ayyukan alheri, bawai ka zauna kullun kana zaman Majalisa, ko buɗe social media shikenan ba. Duka wannan ba zai tserar da kai ba, kuma ka sani za’a tambaye ka kan wannan lokaci da aka baka.

Muyi amfani da rayuwar mu kafin mutuwar mu: ko meye zamuyi a rayuwa zamuyi shi ne idan muna da rai, da zarar mun mutu to wannan damar ta kuɓuce kenan, Kuma babu wani lada da zamu samu sai dai daga ta hanyoyi uku.

  • Sadaƙa mai gudana(Misali mutum ya tone rijiya, ko ya gina makaranta….)
  • Ilimi wanda ake amfan dashi
  • Yaro na gari ya rinƙa yi mana Addu’a. II ji

Wa’innan hanyoyin sune kaɗai zamu iya samun lada dasu bayan mun mutu.

Mai hankali shine wanda yayi amfani da duniyar sa wurin gina lahirar sa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories