Hadisi: Abubuwa uku da Allah baya so bayinsa su aikata

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Akwai abubuwa guda uku da Allah maɗaukakin sarki baya so bayinsa su aikata su. Gasu kamar haka:

1. Jita Jita(Ance Yace): Allah baya son yaɗa jita jita, da yawan magana da bashi da fa’ida. duk abinda mutum yaji yayi bincike kafin ya yaɗa shi, in kuma ba alheri ba ne koda ya tabbatar da ingancin sa to ya kame bakin sa shine yafi alheri.

2. Salwantar da dukiya(Almubazzaran ci): Allah baya son Almubazzaran ci, Salwantar da dukiya ba ta hanyar da shari’a ta yarda ba. Domin Masu almubazzaranci ƴan uwan shaiɗanu ne kamar yadda Allah ya faɗa a Alƙur’ani. Suratul Isra: 27

3. Yawan Tambaya: Allah baya son yawan tambaya cikin abinda bashi da amfani na duniya ko lahira, da yawan tambayan Mutane kan sha’anin Rayuwar su, ko tambaya ta Addini wanda bata da amfani.

An rawaito daga Mugira Bin Shu’uba Allah ya ƙara masa yarda daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Lallai Allah yana Ƙi muku abubuwa uku; Ance sunce(Jita Jita), salwantar da dukiya, yawan Tambaya.

Sahihul Bukhari: 1477

Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: