Da Zikirin Allah ne zuciya take samun natsuwa

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A wannan lokaci na Annoba Musulmi yana buƙatar ya samu natsuwa wanda itace zata sa ya rinƙa fahimtar abubuwa yadda ta dace, sannan kuma natsuwar zata bashi damar tsaya wa kan tafarkin addinin Muslunci a irin halin da ake ciki. Babu abinda zai taimaka wa Musulmi ya cimma wannan buri face zikirin Allah. Allah yace:

الا بذكر الله تطمئن القلوب

Ku saurara kuji, da Ambaton Allah ne zuciya take samun natsuwa.

Ya dace Musulmi ya lazimci Zikirin Allah Musamman zikirin kariya da kuma Istigfari da Salatin Annabi, sannan ya guje wa yaɗa jita jita da surutai wanda basu da kan gado, ko kuma yaɗa labarai da suka danganci wannan Annoba sai dai inya zamto acikinta akwai bayanai ne da zasu taimaka wa mutane wurin kare kansu ko kuma labarai makamantan haka, amma labarai da suka shafi adadin mutanen da suka kamu da wannan cuta, ko kuma yadda cutar take kisa ya kamata mu kame ga barin yaɗa ta domin bata da amfani, wanda ke son samun wannan labarai ya iya bibiyar hukumomi da fitar da wannan bayanai ya rataya akansu.

Kada mu mance cewa duk abinda ya sami Mumini alheri ne, kuma babu abinda zai sameshi sai abinda Allah ya ƙaddara masa, sannan mu sani cewa Mumini baya ɗebe tsammani. Allah Maɗaukakin sarki ya kawo mana ƙarshen wannan Annoba ya kuma jiƙan Ƴan’uwanmu Musulmai da suka rasa rayukansu sakamakon wannnan Annoba. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories