Ya Musulmi ya dace yayi lokacin da aka samu Annoba?

Kamar yadda musulmi ya sani ne cewa wannan Rayuwa dole a samu jarabawa.

Dole Allah ya jarabcemu cikin rayukanmu da jikunanmu da kuma dukiyoyinmu kamar yadda ya bada labari.

ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنفس والثمرات وبشر الصابرين

Haƙiƙa zan jarrabeku da wani abu na tsoro, da kuma yunwa, da Salwantar dukiya da rayuka da ƴaƴan itace.

Daga cikin wa’innan musibu da Allah yake jarabtar bayi dashi akwai Aukuwar Annoba, Wanda zakaji lokaci zuwa lokaci tana aukuwa ayi asarar rayuwa da dama da kuma dukiyoyi.

Me ya dace Musulmi yayi idan Annoba mai yaɗuwa ta auku a gari?

Kamar yadda muke jin labari cewa akwai Annobar Cutar Lassa fever da ta auka wa wasu jahohi a Nigeria, kuma ita wannan Annoba tana da saurin ɗauke rayuwar wacce ta kama. Toh me ya dace muyi?

Ga kaɗan daga cikin abinda ya dace Musulmi yayi domin kare kansa:

  • Neman tsarin Allah: babu abinda yafi ƙarfin Allah, shi ya sauƙar da wannan Annoba kuma shi zai iya kawar dashi, kuma ya kiyaye wanda ya ga dama da adalcinsa. Sabida haka abinda ya dace musulmi ya fara yi shine ya nemi tsarin Allah daga wannan Annoba da ta auku. Akwai addu’oi da dama wanda mutum zai iya yinsu. Kamar Azkar na safe da yamma, Azkar na bacci, Azkar na fita daga gida da sauransu. Wa’innan Azkar ɗin kariya ne ga Mutum, sannan kuma mutum ya yawaita addu’an neman Allah ya kareahi.
  • Neman ilimi game da wannan Annoba da hanyoyin kariya: a lokacin da mutum yaji labarin aukuwar Annoba toh ya hanzarta domin sanin yaya take, ya akeyi a kamu da ita? Sannan ya zaiyi ya kare kansa. Hakan na da mahimmanci matuka, zai iya samun wa’innan bayanai ne wurin hukumomi ko ƙungiyoyi da wayar da kan Al’ummah ta rataya akansu. Amma mutum ya guji ɗaukar magana daga ko wani wuri domin a irin wannan lokaci ana samun jita jita suna yawaita. Sai mutum ya kiyaye yaɗa jita jita, da kuma aiki da ita.
  • Idan Annoba ta auka wa inda yake toh kada ya fice daga wurin, haka nan kuma idan ta auku a wani wuri ne kada ya shiga wurin har sai Annobar ta kau: wannan yana daga cikin hanƴar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da Al’ummarsa da suyi lokacin da aka samu Annoba, wanda kuma wannan tsari yanzu da dama ana amfani dashi a duniyance. Ta yadda in Annoba ta auka wa wani gari hukumomi sukan iya ƙoƙarinsu domin hana mutanen wannan yanki fita, sannan kuma suna hana wasu daga waje shiga, domin a samu a magance annoban cikin sauƙi.

An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:

Idan kukaji labarin Annoba a wata gari to kada ku shigeta, haka nan in kuna cikin garin da ta auku toh kada ku fice daga cikinta.

Bukhari: 5728.
Muslim: 2218

Wannan tsari zai taƙaita yaɗuwar cutar domin bada damar a Shawo kanta cikin sauƙi.

Allah ya ɗaɗa kare mu.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: