Ba jarumta bane jefa kai zuwa ga halaka

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Ahmad Shawki yana cewa:

إن الشجاع هو الجبان عن الأذى … وأرى الجريء على الشرور جبانا

Haƙiƙa Jarumi shine wanda ke zama rago wurin auka wa abinda zai cutar dashi, Sannan ina ganin mai auka wa sharri shine cikakken matsoraci

Shi Addinin Musulunci yazo da kiyaye abubuwa guda biyar masu mahimmanci. Wa’innan abubuwa sune:

  • Kiyaye Addini
  • Kiyaye rayuka
  • kiyaye hankali
  • kiyaye dukiya
  • Kiyaye mutunci
  • Kiyaye nasaba

Kiyaye wa’innan abubuwa na da mahimmanci matuƙa acikin addinin Allah, shiyasa in kayi lura cikin shari’ar Allah zaka ga ana basu kulawa sosai.

Sabida haka ne bashi halatta Musulmi ya jefa kansa zuwa ga halaka, koda hakan da sunan addini ne. Allah yace

ولا تلقوا بأيديكم إلى التهلكة

البقرة: ١٩٥

Kada ku jefa kanku zuwa ga halaka

Duk da wannan ayah ta sauƙa ne kan bada sadaƙa don ɗaukaka kalmar Allah, sai dai tana shafar ko wani irin jefa kai zuwa ga halaka, ta ƙin taimaka wa addinin Allah, ko kuma ta aukawa cikin haɗari da gangan.

A yanzu muna cikin wani lokaci ne na jarabawa ta yadda wannan mummunan Annoba ta Corona Virus ta game duniya, a dalilinta wasu hukumomi a ƙasashe da dama sun kawo wasu dokoki masu tsauri, kaman hana zuwa kasuwanni, hana sallar jam’i, hana Sallar juma’a.

Kuma da yawa daga cikin maluman musulunci sun yarda, sun kuma bada fatawar cewa ya halarta a dakatar da jam’i da kuma sallar juma’a sabida hakan ka iya jawo ƙara yaɗuwar wannan cuta ya kuma jefa rayukar mutane zuwa ga halaka. Kuma abune sananne a addini cewa ana gabatar da tunkuɗe abu mai cutar wa gaban abu mai janyo fa’ida. Sunyi nazarin wannan Mas’ala a mahanga ta Shari’a suka ga ya dace kowa yayi sallah a gidansa.

Amma sai dai wannan fatawa ba dole bane ta zamto ta game ko wani ƙasa ko yanki, domin akwai ƙasashe da wannan cuta bai shiga ba, akwai ƙasashe da ya shiga amma bai game ko ina ba, ta yadda akwai wasu yankuna da baije musu ba, toh anan in Maluman wannan yanki sukayi zama suka ga cewa ya dace su ci gaba da yin Sallolinsu cikin jam’i toh baza ace basuyi daidai ba, sabida kamar yadda aka sani ne cewa fatawa takan canza daga wuri zuwa wuri, ko daga lokaci zuwa lokaci.

Amma in ya zamto cewa a yankin da kake koda wannan cutar bai yaɗu ba, amma duk da haka sai hukuma ta wannan yanki ta bada dokar hana wannan salloli da akeyi sabida riga kafi, ko kuma wasu dalilai tasu, koda ko wannan dalilai da suka bayar ta saɓawa taka toh abinda yafi dace wa shine ka kame ga barin fito na fito dasu, sabida hakan ka iya janyo zubda jinin Musulmi da kuma ci musu mutunci wanda wannan bashi daga cikin abubuwa da shari’a takeso.

Sabida haka kai mabiyi, koda kaji wani Malaminka ya umarce ka da kayi fito na fito da gwamnati kan hana sallah toh ka sani haƙiƙa yana jefa ka ne zuwa ga halaka, kuma bashi halatta kayi masa biyayya wurin saɓon Allah sabida Allah yayi hani ga jefa kai zuwa ga halaka.

Ya dace muyi haƙuri mu danne zuciyarmu, mu sani cewa babu alheri cikin fito na fito da gwamnati a yanzu, domin babu abinda zai janyo mana sai ƙasƙanci da asara da koma baya.

Muna roƙon Allah ya kiyaye mu, ya kuma kawo mana ƙarshen wannan musiba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories