Ladduban Zaman Majalisa

Addinin Musulunci Addini ne wanda ya ƙunshi komi aciki. Duk wani abinda Musulmi yake buƙata yana cikinsa.

a yau zamuyi magana ne kan Hukuncin Zama a Majalisa da kuma Ladduban zaman.

Hukuncin Zama a Majlisa: Zaman Majalisa Halal ne, Amma kuma barin zaman shi yafi alheri, domin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi gargaɗi ga masu zama akan hanya(Zaman Majalisa) kamar yadda Hadisin da zamu kawo zaiyi bayani.

An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

إِيَّاكُمْ وَالجُلُوسَ علَى الطُّرُقَاتِ، فَقالوا: ما لَنَا بُدٌّ، إنَّما هي مَجَالِسُنَا نَتَحَدَّثُ فِيهَا، قالَ: فَإِذَا أَبَيْتُمْ إِلَّا المَجَالِسَ، فأعْطُوا الطَّرِيقَ حَقَّهَا، قالوا: وَما حَقُّ الطَّرِيقِ؟ قالَ: غَضُّ البَصَرِ، وَكَفُّ الأذَى، وَرَدُّ السَّلَامِ، وَأَمْرٌ بالمَعروفِ، وَنَهْيٌ عَنِ المُنْكَرِ.

Bukhari: 2465

Fassara:

Ina horanku da zama akan tituna(Ma’ana a gefen tituna) sai sukace Babu yadda muka iya, itace wurin zaman mu da muke haɗuwa mu tattauna, sai Annabi yace: idan har kunƙi sai kun zauna to ku baiwa hanya haƙƙinta, sai sukace menene haƙƙin hanya? Sai yace: Rintse ido, kamewa ga barin cutar da mutane, mayar da Sallama, umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

Wannan hadisi yana nuna cewa Zama a majalisa ba haramun bane, amma rashin zaman shi yafi alheri, sabida Fitintinu da mutum zai iya jefa kansa aciki.

Acikin wannan hadisi Annabi yayi bayanin Ladduban zama a majalisa kamar haka:

  1. Rintse idanu: kada mutum ya sake idanunsa komi ya wuce sai ya kalla, Musamman kallon mata, ko kuma Mutum ya rinƙa sanya idanunsa kan abinda Allah ya azurta mutane dashi na ababen hawa da makamantansu.
  2. Kamewa ga barin cutar da mutane: Idan kana zama a majalisa to ka kiyaye gulman mutane, ko kuma cutar dasu da idanuwanka ta yadda zaka ƙura musu idanu har ya zamto sun takuru, ko kuma ya zamto hanyar a matse take kuzo ku ƙara matse ta.
  3. Mayar da Sallama: duk wanda yayi muku sallama kuna zaune a Majalisa to dole ku maida masa da sallamar.
  4. Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna: hakanan Duk masu zaman majalisa ya wajaba a garesu su rinka umarni da kyakkyawa da hani da mummuna acikin Majalisar tasu da kewayen da suke zaune, misali wani yazo yana aikata abinda bai dace ba to dole su hana shi koda ko a cikinsu ne.

Wa’innan sune Ladduban zama a majalisa, kamar yadda mukayi bayani a baya cewa Rashin zaman shi yafi alheri, domin mafi yawancin majalisoshi a wannan zamani basu kuɓuta daga wa’innan abubuwa da Annabi ya lissafa. Ko dai ya zamto ana gulman mutane, ko kuma ana kallon mata masu wuce wa, ko kuma ya zamto basu amsa sallama, ko kuma basu umarni da kyakkyawa suna hani da mummuna. Sabida haka sai mu kula mu kiyaye, mu lazimci gidajenmu sai dai in akwai wata buƙata ta zama a wurin.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: