Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 4: Wanda ya dauki nauyin kula da Annabi bayan mutuwar Mahaifiyarsa

Shekara kafin Hijira: 48

Shekarar Miladiyya: 575


Kamar yadda ya gabata munyi bayani cewa mahaifiyar Annabi ta rasu yana da shekaru shida a rayuwarsa, ta rasu ne a hanyarsu ta dawo wa daga ziyara da takai zuwa ga ƴan’uwanta. Ta rasu a wani wuri da ake kira Al’abwa.

Toh bayan rasuwarta Ummu aiman ita taci gaba da rainon Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Sai kuma kakansa Abdulmuddalib yaci gaba da ɗaukan nauyinsa.

Abdulmuddalib ya kasance mai Daraja acikin mutanensa, ya kasance yana da kyauta. Kuma ya kasance shine ya ɗau nauyin kula da masu zuwa hajji a lokacin jahiliyya bayan Rasuwan mahaifinsa Hashim ɗan Abdu Manaf. Abdul Muɗallib ya kasance yana son Annabi Sallallahu alaihi Wasallama so mai tsanani. Yana ƙaddamar dashi kan sauran ƴaƴansa

Ibn Ishaq yace:

Manzon Allah ya kasance tare da kakansa Abdulmuddalib bayan rasuwar mahaifiyarsa. An kasance ana sanya wa Abdulmuddalib shimfiɗa a ƙarƙashin inuwar ka’abah sai ƴaƴansa su zauna a gefen shimfiɗar har sai ya fito. Babu mai zama akan shimfiɗar sabida girmama shi Abdulmuddalib ɗin. Amma Manzon Allah yakan zo ya zauna akai. Sai suyi ƙoƙarin hanashi zama akai. Da zarar Abdulmuddalib yaga haka sai yace musu kubar min ɗa na. Wallahi yana da sha’ani. Sai ya zaunar da Annabi akan shimfiɗar sa. Ya shafi bayan Manzo Allah.

Kuma yana farin cikin kan abubuwan da Manzon Allah yake aikatawa. Sannan Abdulmuddalib baya cin abinci har sai yasa an kawo masa Annabi kusa dashi.

Lokacin da mutuwa tazo wa Abdulmuddalib sai yayi wasiyya wa ɗansa Abu ɗalib da ya kula da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Sai mun haɗu a kashi na Biyar.

Donate to support Us. May Allah reward You with Jannah
Account Number: 3077875210
Account Name: Mukhtar Muhammad
Bank: First Bank Nigeria
You can also Click Here to Donate Online

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You may use these HTML tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>

%d bloggers like this: