Tarihin Annabi fitowa ta 3: Mutuwar Mahaifiyar Annabi

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mutuwar Mahaifiyar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kuma ɗaukan nauyin rainonsa da Ummu Aiman tayi


Shekara kafin hijira: 48


Shekarar Miladiyya:575


lokacin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yakai shekaru shida a Rayuwarsa mahaifiyarsa Aminatu Bintu wahab ta ɗaukeshi domin kai ziyara wa ƴan’uwanta Banu Adiy Bin Najjar. Lokacin da tayi wannan tafiya akwai tare dasu Ummu Aiman wacce itace take rainon Manzon Allah. Sunanta shine ” Barakah bintu tha’alabah bin Hisn”. Ta kasance baiwa ce ga Mahaifin Annabi.

Sunyi zaman wata guda awurin ƴan’uwan Mahaifiyar Manzon Allah. Bayan sun kammala ziyararsu sai suka shirya dawowa, a hanyarsu ta dawowa a wani wuri da ake ƙira “Al-abwa” . Sai Allah yayi wa mahaifiyar Manzon Allah rasuwa. Sai Ummu ayman ta dawo dashi zuwa gida. Ummu ayman ta kasance tana son Annabi Sallallahu alaihi Wasallama sosai kuma tana bashi kulawa tana kuma tausaya masa. Manzon Allah ya kasance yana mata biyayya kuma yana kyautata mata. Lokacin da Annabi ya Girma sai ya ƴanta ta daga bauta, sannan ya aurar da ita zuwa ga Zaid bin Haritha. Ummu ayman ta rasu bayan rasuwar annabi da wata biyar


Wannan Tarihi ina tsaƙuroshi ne daga Mausu’ah ta Tarihi ta “dorar.net” domin karantawa cikin harshen larabci Danna nan. Domin yin gyara Danna nan

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories