Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 6: Tafiyar Annabi da baffansa zuwa Sham

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Shekara kafin hijira: 42


Shekarar Miladiyya: 581


Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yakai shekara goma sha biyu. Baffansa Abu Ɗalib wanda shine yake ɗaukan nauyin annabi kaman yanda mukayi bayani a baya. Ya ɗauki annabi Sallallahu alaihi Wasallama zuwa Ƙasar Sham acikin tawagar ƴan kasuwa. Lokacin da suka isa Busra sai tawagar ta yada zango domin hutu sai manzon Allah da baffansa suka wuce kusa da wani fada(Malamin Kirista) na Kiristoci.

Wannan malami yana da ilimin injila sosai da kuma sifofin Annabin ƙarshen zamani. Lokacin da wannan fada yaga Annabi sai ya fara nazarin halayyarsa ya kuma cigaba da yi wa Annabi magana. Bayan haka sai ya juya zuwa ga Abu ɗalib yace masa Meye matsayin wannan yaro a wurinka? Sai Abu ɗalib yace: ɗana ne. Dama Abu ɗalib ya kasance yana kiran Annabi da ɗansa domin tsananin son da yake masa da kuma tausayinsa da yake yi. Sai wannan fada yace wannan ba ɗanka bane. Kuma bazai yiwu ace mahaifin wannan yaro yana raye ba. Sai Abu ɗalib yace ɗan ɗan’uwa na ne. Sai fadan yace meye labarin mahaifinsa? Sai Abu ɗalib yace: ya rasu lokacin mahaifiyarsa tana da cikinsa. Sai fadan yace kayi gaskiya. Yace Ka koma dashi zuwa gida ka guji Yahudawa su ganshi. Domin idan suka ganshi toh zasu cutar dashi. Kuma wannan yaro na ɗan’uwanka akwai babban lamari da zai faɗo kansa. Sai Abu ɗalib yayi sauri ya koma dashi zuwa Makkah.

Thirmidi ya rawaito:

Lokacin da Abu ɗalib ya fita da Manzon Allah zuwa shaam tare da Manyan Quraishawa. lokacin da suka kusa da wannan Malamin kiristoci Bahira Sai suka yada zango akusa dashi. Sun kasance in suna tafiya in sukazo wuce wa kusa dashi baya kulasu amma a wannan lokacin sai ya fito. Suna cikin Sauƙe kayansu don hutu da hutar da ababen hawansu sai shi kuma wannan fada yana ta dudduba su har yazo wurin Annabi ya kama hanunsa sai yace: Wannan shine shugaban halittu baki daya. Wannan Manzon Allah ne, Allah zai turo shi domin rahama ga halittu. Sai wa’innan dattawa na Quraishawa suka ce masa waye ya baka wannan labari? Ya akayi ka sani? Sai yace; lokacin da kuka dumfaro wannan hanya babu wani dutse ko bishiya face ya kasance yana yi masa sujjada. Kuma basu yi wa kowa sujjada sai Annabi. Kuma na ganeshi ne da Hatimin Annabta dake bayansa a ƙasan kafaɗarsa. Sai wannan fada ya dawo yayi musu abinci, ya kawo musu. Ya tura aka kira Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Lokacin da ya ƙaraso sai ya samu mutane sun rigayeshi zuwa ga inuwar bishiya. Lokacin da Manzon Allah ya zauna sai wannan inuwar ta karkata zuwa gareshi. Sai Wannan fada yace wa Wa’innan Dattawan Quraishawa ku dubi yadda wannan inuwar bishiya ta karkata zuwa gareshi. Sai wannan fada ya fara nema daga garesu cewa kada su tafi dashi zuwa Rum. Domin idan romawa suka ganshi zasu kashe shi. Ana cikin wannan yanayi sai ga wasu su bakwai daga cikin Rumawa sunzo zuwa gareshi. Sai ya tarbesu yace me ya kawo ku? Sai sukace munji cewa wannan Annabi da za’a turo na ƙarshen zamani ya fito zuwa fatauci acikin wannan watan. Babu wata hanya face an tura mutane domin su binciko shi. Muma an turo mu ne zuwa gareka domin binciko shi. Sai yace shin akwai wani wanda ya fiku wanda ke biye daku? Sai suka ce anbamu labari ne cewa yana kan wannan hanya taka. Sai yace shin kuna ga abinda Allah yaso ya wakana akwai wanda ya isa ya hana aukuwar sa? Sai suka ce A’a. Sai yace to kuyi masa mubaya’a. Ku kuma zauna tare dashi. Sai wannan fada ya tambayi Wa’innan Dattawan Quraishawan shin wanene Mai kula da Annabi acikin ku? Sai aka nuna masa Abu ɗalib. Sai yayi ta baiwa Abu ɗalib haƙuri har sai da ya mayar dashi zuwa Makkah ya fasa tafiyar.


Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories