Al Mahdiyyul Muntazar

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bismillah Wassalatu wassalamu Ala Rasulillah wa ba’ad.

wanene Al-Mahdi wanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi bushara da zuwansa a ƙarshen zamani?

Hadisai sun tabbata daga Annabin tsira Sallallahu alaihi Wasallama kan zuwan Mahdi a ƙarshen zamani, wanda wannan hadisan wasunsu sun isa haddin mutawatir.

Daga cikin hadisan da sukazo a wannan babi akwai hadisin Abdullahi ibn Mas’ud wanda Abu dawud, da Turmithi da ibn Hibban sun rawaito shi.

Annabi yace:

Idan da duniya zatazo ƙarshe ya zamto babu wani ragowar rana sai rana ɗaya, sai Allah ya sanya wannan ranar ta zamto doguwa ta yadda zai turo wani mutum daga tsatso na, ko daga iyalan gidana, sunansa zai dace da suna na, haka nan sunan mahaifinsa zai dace da sunan mahaifina, zai cike ƙasa da adalci kamar yadda aka cike ta da zalunci da ƙetare iyaka.

Acikin wannan hadisi Annabi ya nuna cewa Mahdi zai zo, kuma Sunansa shine Muhammad ibn Abdullah.

an samu wasu ɓangare masu cewa Mahdi da Annabi yayi bushara da zuwansa shine: Annabi Isa ɗan Maryam. Suna riƙo da wani hadisi wanda bai inganta ba, na cewa: Babu mahdi sai Isa. Sannan kuma suna amfani da wasu tawilce tawilce domin kore zuwan shi Al- Mahdi. Amma a haƙiƙanin gaskiya wannan magana tasu bata kan turbar da ta dace. Domin kamar yadda mukayi bayani a baya hadisan da sukazo kan batun zuwan mahdi hadisai ne masu ɗinbin yawa, kuma akwai ingatattu da yawa aciki. Kuma acikin hadisan akwai wanda yake nuna zuwan Annabi Isa daban zuwan Al- Mahdi daban.

Aqeedar zuwan Mahdi yana daga cikin manyan abubuwa da aka sami tsaɓani tsakanin Shi’ah da Sunnah akai

Kamar yadda ya gudana wannan shine Aqeedar Ahlussunnah kan Al – Mahdi:

Sunansa Muhammad ibn Abdullahi. Kuma za’a haifeshi nan gaba, zai zo ne a ƙarshen zamani domin ya cike ƙasa da adalci. Kuma shi daga cikin zuriyar Annabi yake.

Amma awurin ƴan Shi’a mahadin su ya banbanta da na Ahlussunnah.

Mahdi awurin ƴan shi’ah Imamiyyah sunansa Muhammad ibn Hasan Al-Askari. Yanzu haka an haifeshi yana nan ya ɓuya a wani ƙogo a Samarra dake ƙasar iraq tun yana ƙarami. Tun daga lokacin ba’a sake jin labarin sa ba, kuma ba’a sake ganinsa ba. Sukan je wurin lokaci zuwa lokaci domin nemansa da ya fito.

Wannan shine taƙaitaccen bayani kan Al-Mahdi Al Muntazar.

Aqeedar da ya dace musulmi ya ƙudurce shine abinda ya tabbata a ingatattun hadisai wanda yayi nuni da zuwan Al-Mahdi. Amma ba’a san lokacin da zai zo ba, sai lokacin da Allah yaga daman zuwansa, kuma ba’a haifeshi ba a yanzu.

Allah yasa mudace.

Domin neman ƙarin bayani zaka iya duba lekca da Sheikh Albani Zaria yayi kan wannan batu mai Suna Al-Mahdi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories