Ku tambayi masana ilimi inku baku sani ba

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yana daga cikin umarnin da Allah Subhanahu wa ta’ala yayi wa Musulmai cewa idan wani abu ya shige musu duhu to su tambayi wa’inda suke da ilimi kan wannan abin. Kaman yadda ya faɗa cikin Suratul Anbiya aya ta 7.

فاسألوا أهل الذكر إن كنتم لا تعلمون

Allah ya bada labari kan aiko annabawa. Ta yadda yana aiko annabawa ne cikin mutane kuma mazaje. Ya kuma faɗa wa mutanen Makkah cewa su tambayi masana ilimi da littafan da Allah ya turo kafin zuwan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Sune yahudu da nasara zasu basu labarin gaskiyar wannan zance.

Sabida haka ya dace Musulmi ya ɗauki wannan umarni yayi aiki da shi cikin rayuwarshi baki ɗaya, musamman kan abinda ya shafi addininsa. Domin addini shine babban abinda mutum yake tinƙaho dashi wanda in ya rasa to yayi babban rashi, kuma yayi asara duniya da lahira.

Annabi Sallalahu alaihi wasallam ya bada labari cewa a ƙarshen zamani za’a ɗauke ilimi, kuma jahilci zai yawaita kamar yadda Anas bin Malik ya rawaito

من أشراط الساعة أن يرفع العلم ويثبت الجهل

البخاري: 80
مسلم: 2671

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

Daga cikin alamun ƙaratowar tashin Al-Qiyama shine: za’a ɗauke ilimi, sannan jahilci zai yawaita

Wannan abu ne da yake faruwa a wannan zamani, ta yadda ya zamto kowa yana magana kan addini koda ko bashi da ilimi kan abinda yake faɗi. Ya halaka ya kuma halakar.

To a irin wannan lokaci mai tsarƙaƙiya da fitintinu sukayi yawa ya dace Musulmi ya kula sosai, ya kula da addinin sa, ya kauce wa duk wani hanya da zai sa addininsa ya samu matsala.

Akwai da yawa daga cikin shaiɗanun mutane masu yaɗa shubuhohi wa mutane domin su ɓata musu addininsu. Dole ne Musulmi ya kauce wa irin wa’innan mutane, sannan in yana da wani matsala a addini ya tabbata wanda zai tambayeshi yana da ilimin mai ƙarfi a addini. Kamar yadda ba’a tambayan kowa kan harkar kiwon lafiya sai Likita, haka nan ba’a tambayar kowa kan harkar Addini sai malami. Malamin kuma ƙwararre.

Sannan a irin wannan lokaci ya wajaba ga Musulmi ya zamto yana da matashiya kan ilimin addini. Domin hakan ne zai bashi daman banbance tsaƙanin ƙarya da gaskiya.

Sannan kuma ka sani duk cewa yawancin shubuhohi da ake yaɗa wa cikin wannan zamani namu an yaɗa su a lokuta da suka gabata, kuma Maluman Musulunci sunyi bayani akansu, bayani mai gamsar wa, ƙarancin ilimi da rashin bincike yake sa da yawa daga cikin masu tayar da irin wa’innan shubuhohi a wannan zamani sukeyi. Kamar yadda duk wani hadisi da zaka gani, ko wani ayah da zaka karanta ka sani cewa maluma magabata sun san dasu, sun karanta su, kuma sunyi bayani akansu. Abinda kawai ya rage sai dai ka koma littafan su ka karanta, ko kuma ka sami Malami yayi maka bayani.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories