Ramadaniyyat: 1445 [2]‎ Rabbaniyyun: Ilimi da Malanta

Danna nan domin shiga group na karatu Online

2.0. Kyautata Niyya:‎

‎2.1. Kyautata niyya watau ikhlasi, ginshiƙi‏ ‏ne na kowace ibada a ‎Musulunci. Ilimi ibada ce babba, domin da shi ne ake sanin Allah da ‎annabawansa da abin da ya ya saukar da sauran shikashikan imani. Mai ‎neman ilimi shi ne farkon wanda za a yi tsammanin zai tsarkake niyyarsa, ‎ya kyautata nufinsa tsakaninsa da Mahaliccinsa, ya nemi ilimi don Allah, ‎ba don wata manufa ta ƙashin kansa ba. Idan ya yi haka, to da ma hakan ‎ake kyautata masa zato zai yi tun farko. Amma idan ya yi akasin haka, to ‎lalle al’amarinsa zai yi matuƙar muni, zai zamanto kamar yadda Hausawa ‎kan ce, ‘ana zaton wuta a maƙera sai kuma kwatsam ga ta a masaƙa’.‎

‎2.2. Hadisi mai matuƙar razanarwa da ban tsoro ga ɗalibin ilimi ko ga ‎malami, shi ne hadisin da Ka’abu ɗan Malik ya ruwaito daga Annabi ‌‎(SAW) yana cewa, “Duk wanda ya nemi ilimi domin ya yi kafaɗa da ‎kafaɗa da malamai, ko kuma don ya yi jayayya da jahilai, ko kuma don ‎ya jawo hankulan mutane zuwa kansa, to wannan Allah zai shigar da shi ‎wuta”. [Tirmizi, #2654, Ibn Maja, #253]. A hadisin Jabir ɗan Abdullahi, ‎Annabi (SAW) cewa ya yi, “Kada ku nemi ilimi domin kawai ku riƙa yi ‎wa malamai fariya da shi, ko domin ku yi jayayya da jahilai da shi, ko ‎kuma don ku jagoranci majalisai da shi. Duk wanda ya yi haka, to wuta ta ‎tabbata gare shi, wuta ta tabbata gare shi”. [Ibn Hibban, #77].‎

‎2.3. Babban abin da zai jawo haka, kamar yadda malamai masu sharhin ‎hadisai suka faɗa, shi ne rashin tsarkake niyya da neman suna da fariya da ‎kuma neman abin duniya. Waɗannan duka ɓacin niyya ce take haddasa ‎faruwarsu. Neman ilimi don kawai samun tagomashin duniya alama ce da ‎ke nuna mutuwar zuciya. Malik ɗan Dinar ya tambayi Alhasan al-Basri, ‌‎”Mece ce uƙubar malami?” Sai ya ce masa: “Mutuwar zuciya”. Sai ya ‎tambaye shi, “Mene ne kuma mutuwar zuciya?” Sai amsa masa da cewa: ‌‎”Neman duniya da aikin lahira”. [Ahmad, az-Zuhd, 265].‎

‎2.4. Zahabi, babban masanin tarihin Musuluci yana cewa: “Magabata sun ‎kasance masu neman ilimi don Allah, sai wannan ya sa suka ɗaukaka, ‎suka kuma zamanto shugabanni abin koyi. Wasu kuma suka fara neman ‎ilimi ba don Allah, suna tsaka da nemansa sai kawai suka farka, suka yi ‎wa kansu hisabi, daga nan sai iliminsu ya ja su zuwa ga ikhlasi. Kamar ‎yadda Mujahid da waninsa suke cewa: “Mun nemi ilimi ba tare da wata ‎niyya ta a zo a gani ba, sai daga bisani Allah ya arzuta mu da kyakkyawar ‎niyya. Wasu kuma cewa suka yi: “Mun nemi ilimi ba don Allah ba, amma ‎ilimin ya ƙi, sai dai ya zamo don Allah”. [Zahabi, Siyarun Nubala’, juz. 7, ‎sh. 152].‎

Za mu ci gaba in sha Allah…‎

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories