Maqala

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma – Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

 1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su zamanto jarraba wa ga bayinsa, domin ya bayyana wadanda suka fi kyautata ayyukansu. Wajibi ne ga duk wani Musulmi ya rika halarto da wannan ma’ana a zuciyarsa duk sanda ya ga an shiga wani yanayi bako a rayuwa. Ya yi kuma kokarin cinye wannan jarrabawa.
 2. Hukumar samar da takardun kudade karkashin babban bankin Kasa, tare da sahhalewar Shugaban Kasa sun yi tunanin sake fasalin wasu takardun kudaden Nigeria domin wasu maslahohi da suka hango da kuma magance wasu matsaloli. Muna musu kyakkyawan zato cikin wannan kuduri nasu, muna kuma fatan a yi nasara cikin hakan.
 3. Amma duk da haka, wajen tabbatar da waccan kyakkyawar manufa, talakawa a Nigeria, sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai ban tausayi, musamman a kauyukanmu na Arewa. Don haka muna rokon hukumar da wannan abu ya shafa da su duba halin da Jama’a suke ciki, su amsa kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin da suka saka na dakatar karbar tsofaffin kudi, ko kuma su yi wa tsarin gyaran fuska, don fitar da al’umma daga wannan kangi mawuyaci.
 4. Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukakewa al’umma rayuwarsu ne ta yau da kullum, da kuma sama musu walawala a harkokinsu, da guje wa jefa su cikin tsanani da wahalhalu.
 5. Fatanmu hukuma za ta dubi wannan lamari ta kuma yi abin da ya dace. Allah ya musu kyakkyawan jagoranci, ya ba mu zamanan lafiya da arzuki mai dorewa a Kasarmu. Amin.

Fatawoyin Rahama By Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo 7th January 2023

Tambayoyi da Amsoshi

 1. Menene hukuncin sanya rigar ‘ graduation’ da ake sanyawa yayin yaye ɗalibai’!
 2. Wanda  aka ɗauke shi  aikin kula da ba da magani a Asibiti (“pharmacist”) amma saboda yana da ƙwarewar yin kaciya ma yara, aka sa ya rinƙa yi ma yara kaciya da aka kawo Asibiti – ya hallata ya karɓi kuɗin da ake bayarwa na yin kaciyar?
 3. Wasu kaddarori ake fitar musu da Zakka?
 4. Menene hukuncin wanke hannu a kwano kafin da bayan cin abinci!
 5. Hukuncin zuwa kitso wajen matar boka!
 6. Hukuncin wanda ya yi parking mota wani mai babur ya zo ya buge ƙofar mota  ya je gaba ya buge wata mota ya mutu!
 7. Ya hallata mutum ya yi hoto na mussaman na mahaifiyar sa bayan rasuwarta?
 8. Mai Sallar Isha’i zai iya bin mai Sallar Tarawih da yake raka’a huɗu a haɗe?
 9. Mamu da yake bin Liman a sallar da ake bayyana karatu zai sake raka’a da ya manta karanta mata Fatiha?
 10. Wanda ya manta ya karanta Sura a inda ake karanta Fatiha kawai ko ya karanta Fatiha ba tare da sura ba a inda ake karanta su – zai yi Sujjadar Rafkanuwa?
 11. Me mutum zai ce in ya ji mai kiran sallah yana cewa ‘ assalatu khairun minannaum’!
 12. Ya inganta in aka ce’ Hayya Sallah ko Hayya Falah’ Mutum zai ce ‘ Laula Wala Ƙuwata Illa Billa’?
 13. Ya hallata mutum ya yi Sallah a gidansa in ba massalaci a kusa da inda yake!
 14. Wadda mijinta ba ya son ta rinƙa tashi tana sallar dare – ya ya za ta yi?
 15. Mutum zai iya karanta Suratul Ikhlas sau uku a raka’a ɗaya domin samun falala?
 16. Yaya matsayin mace da ta ga jinin da bai yi ja kamar yadda ta saba gani ba?
 17. Wanda ya mutu da janaba wankan gawa zai ɗauke janaban?
 18. Ya tabbata in Annabi ﷺ ya gama huɗuba yana barin Sahabbai su yi tsokaci ko tambayoyi!

DOWNLOAD

Fatawoyin Rahama By Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo 8th January 2023

Tambayoyi da Amsoshi da ke ciki tare da Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON

 1. Iyaye da ba musulmi ba su na da haƙƙin aurar da ‘yar su da ta musulma?
 2. Ya hallata iyaye su bawa mutane biyu damar nemar auren ‘yar su?
 3. Ya hallata mutum ya yi walima in ya samu wani ƙarin girma ko wani alheri na duniya?
 4. Ya hallata yaro ya sayar da geron gidansu domin ya biyawa kansa buƙatunsa?
 5. Wanda aka ba shi aikin raba kaya sai kayan ya saura kuma akwai sharaɗi ba a mayar da ragowar kaya?
 6. Ina matsayin a ɗaura mutum a gurbin ma’aikacin da ya rasu?
 7. Ya hallata mutum ya yi ƙarya rashin lafiya domin kada ya je hidimar ƙasa saboda taɓarewa da ake yi!
 8. Ana iya sutra da mutum?
 9. Jini da yake ɗigowa mai shayarwa zai hana ta ibada?
 10. Shin Lukuman Annabi ne?
  Kuma a ina ya rayu?
 11. Ya kamata Ladan in ya makara ya tarar wani ya fara kiran sallah ya karɓi lasfika ya cigaba da ga in da ya tarar?
 12. Hukuncin sanya Hula!
 13. Hukuncin wanda yake aron kuɗin ajiya!
 14. In aka ba mutun kuɗi ya ci abinci in kuɗin ya saura zai iya amfani da sauran kuɗin?
 15. Hukuncin wanda yake tashi daga wajen aiki kafin lokaci amma yana aikin yadda ya kamata!
 16. Ya hallata mutane da suke raba kaya su fifita kawunan su?
 17. Ya hallata mutum ya ba da ‘account numbansa’ ga wani da zai yi amfani da shi don samun tallafin Gwamnati tare da alƙawarin zai bawa mai account din wani abu?
 18. Hukuncin wanda aka ba shi aikin gadi ba ya samun zuwa Sallar Juma’a
 19. Shin Dujjal zuwan sa zai yi tasiri har da waɗanda suka mutu?
  Sannan Yajuju da Annabi Isa a Dujjal -wa zai fara zuwa?
 20. Wanda yake azumin nafila bai samu ikon yi ba saboda rashin lafiya – zai rama?
 21. Shin wanda ya samu tahiya ya samu jam’i?
 22. Ina matsayin yin iƙama da kuskure?
 23. Idan jinin haila ya ɗauke wa mace a lokacin da ba za ta iya wanka ba za ta iya taimama?
 24. Shin haila na iya zuwa bayan kwana 40 da haihuwa?

DOWNLOAD

Fatawoyin Rahama By Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo 1st January 2023

Lahadi 9/6/1444 – 1/1/2023

Tambayoyi da Amsoshi tare da Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON

 1. Menene ingancin cewa ba a yin Sallar nafila bayan Sallar Ƙasaru?
 2. Hukuncin karɓar ‘overtime’ ba tare da yin aiki da ake biyar wannan ‘overtime saboda da ya yi aikin overtime a zamanin baya amma ba a yi shi ba!
 3. Iyaye za su taimaka wa ‘yar su a gidan aure ko da mijinta yana ƙin haka?
 4. Wanda ya yi Bakancen zai yi azumin kwana uku a kowanni wata in sun fado a ranar Litinin da Alhamis , in azumin kwana uku ba su fado a ranar Litinin ko Alhamis yaya zai yi?
 5. Wanda ya yi bakancen zai yi Azumin Annabi Dawuda (AS) zai iya hutu na wani lokaci? Ko kuma in ya yi tafiya?
 6. Akwai amfani mutum ya yi sammakon zuwa massalacin Jumu’a a in da ake huɗuba da yaren da ba ya fahimta?
 7. Wanda ya yi salla a gida zai iya samun ladan jam’i in zuwa massalaci yana wahalar da shi saboda nisa?
 8. Wanda ya tafi karatu zai iya ƙasaru har ya gama karatu?
 9. Hukuncin ba da kwangila ga matar shugaba!
 10. Ya hallata yin sujjada akan naɗin rawani ko ɓangare na hula a lokacin sanyi ko tsananin zafi!
 11. Yaya mutum zai tsayar da yatsa ya yin Tahiya?
 12. Hukuncin cin abincin da Kirista ya dafa!
 13. In mace ta ba wani dama ya aureta sai bai samu hali ba, shin ta na da laifi in ta aure wani da ya shirya?
 14. Mutum zai iya ƙin taimakawa Mahaifinsa da ba ya kyautata wa Mahaifiyarsa?
 15. Hukuncin wanda ya siyya wa abokinsa giya ba da sani ba!
 16. Ya inganta Allah yana biya wa wasu musulmi bashi ranar Alƙiyama?
 17. Ƙarin haske akan hadisin kowanne abin Haihuwa ana haifar sa ne akan fiɗira
 18. Shin wanda yake gadi a wata ma’aikata wasu suke zuwa suna rashin gaskiya zai iya karɓar kuɗi da ake ba shi in an zo ɗaukan kaya?
 19. Mutum zai iya zuwa Sallah Massalaci da ke nesa da in da yake saboda massalacin da ke kusa suna karanta Alƙunut duk sallar Asuba!
 20. Mutum zai iya Siyan Alƙur’ani ya bayar sadaƙa jariya ga mahaifiyar sa?
 21. Ya ya mutun zai cigaba da biyyaya ga Mahaifiyarsa da ta rasu alhali bai kyautata mata a lokacin da ta ke raye ba?
 22. Wadda mahaifiyar sa ta rasu ake zargin kashe ta aka yi, zai iya bincike ya gano gaskiyar abin da ya faru?
 23. Ya hallata mutum ya koyi Al-ƙur’ani ta hanyar sauraro kadai?

Download