Abubuwan da zai Taimaka wa Musulmi wurin Tsayuwar dare(Qiyamul-layl)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Sallar dare yana daga cikin Ibadodi masu girman falala, kuma ba kowa yake samun dace wa da wannan ibada ba sai wanda Allah ya masa dacewa.

Akwai hanyoyi da ya kamata mutum yabi domin shiga cikin sahun bayin Allah masu tsayuwar dare gasu kamar haka:

  1. Neman taimakon Allah: abu na farko da mutum ya kamata yayi shine ya nemi gudunmawar Allah maɗaukakin sarki domin da taimakon Allah ne mutum zai iya samun damar ya tashi a gaban Allah a wannan lokaci mai matuƙar falala.
  2. Kwanciya da wuri: kwanciya da wuri yana taimaka wa Mutum ya samu bacci wanda zai ishe shi kafin lokacin da zai tashi ya gabatar da ibadodin sa
  3. Cin abinci kaɗan kafin lokacin bacci: yana da kyau mai son ya rinƙa tashi wa Sallar dare ya ci abinci da wuri kafin lokacin baccinsa sannan kuma ya taƙaita cin abinci kada yaci da yawa kafin yayi bacci
  4. Yin Alwala da nafila kafin bacci: Kafin mutum ya kwanta yayi alwala, sannan yayi nafila ko da raka’oi biyu ne ko huɗu sai ya kwanta.
  5. Kwanciya da Niyya: idan mutum zai kwanta sai ya ƙudurce niyyar tashi Sallar dare, hakan zai taimaka wa mutum wurin tashi. haka nan idan Allah ya ga gaskiyar niyyar sa to zai taimaka masa wurin Tashi. Allah ya taimaka mana ya datar damu da tashi Sallar dare

Leave a Reply

Latest updates
Categories