Falalolin Suratul Baqara

Ga kaɗan daga cikin Falalolin Suratul Baqara

  1. Tana korin Shaiɗan: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: ” Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baqara”
  2. Tana bada kariya ga mai karanta ta Ranar Tashin kiyama: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: Ku karanta masu Haskakawannan guda biyu Baqara da Aal Emran, domin zasu zo ranar tashin Alƙiyama kamar Girgije guda biyu a siffar tsuntsaye wanda suke haɗe da juna su tsare mai karanta su, su Zamto Hujja a gareshi”
  3. Samun Albarka da karanta ta: An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: ” Ku karanta Suratul Baqara, Domin riƙo da ita albarka ne, barinta kuma hasara ne”
  4. Girmama wa da Sahabbai suke yi ga wanda ya karance ta: An rawaito daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace: ” Mutum ya kasance idan ya karanci Suratul Baqara da Aal Emran ana lissafa shi daga manya a cikinmu.

Wannn kaɗan kenan daga cikin falalar wannan Surah Mai Albarka, duk maison samun kariya a gidansa da Albarka sai ya lazimci karanta wannan Surah acikin gidansa.

Abinda Anas yake nufi da wanda ya karanci Surar shine: Ya Haddace, sannan ya san Ma’anar ta.

Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: