Addu’ar Saduwa da iyali ko saduwa da Amarya

An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

‏لو أن أحدكم إذا أتى أهله قال‏:‏ بسم الله، اللهم جنبنا الشيطان وجنب الشيطان ما رزقتنا، فقضى بينهما ولد لم يضره

Bukhari: 141

Fassara

Da ɗaya daga cikinku lokacin da zaije wa iyalinsa yace: Ya Ubangiji na ka nesantar da shaiɗan daga garemu, haka nan ka nesantar da shaiɗan daga abinda ka azurta mu dashi. Idan har Allah ya hukunta samun ɗa a tsaƙaninsu ta wannan saduwa da sukayi shaiɗan ba zai cutar dashi ba.

Addu’ar itace:

Allahumma Jannib na-sshaiɗana wa jannibi-sshaiɗana ma Razaqtana.

Yana da kyau Mu kiyaye wannan addu’a, domin yana da matuƙar Mahimmanci, hakanan Wanda zaiyi wannan addu’a yayin saduwa shine Miji.

Allah yasa mudace, ya kuma bamu kariya.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: