Nafilar da Annabi baya bari Sabida Mahimmancin ta

Tambaya: Shin wacce Nafila ce Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yafi kiyaye wa, baya bari ta wuce baiyi ba?

Amsa: Abune sananne cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yafi kowa Ibada, duk da cewa Allah ya gafarta masa zunubansa baki ɗaya, Amma duk da haka an Rawaito ya kan tsaya Sallah har ƙafafuwansa su kunbura, aka tambaye shin meyasa yake yin Haka bayan Allah ya gafarta masa dukkan Zunubansa? Sai yace shin Bazan zamto bawa mai godiya ba? [Sahihul Bukhari: 4836].

Amma acikin Nafiloli da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yake yi akwai Nafila guda ɗaya

wanda yafi maimaita ta, wanda Baya bari ta wuce shi Wannan kuwa itace Raka’ata Alfajr(Raka’oi Biyu na Alfijir) Wanda munyi bayanin Falalolin wannan Sallah, mai son dubawa sai ya duba Wannan rubutu dake ƙasa.

Wannan itace nafila da Annabi yake yawan yinta baya bari ta wuce shi, sabida falalar ta.

An Rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda cewa Annabi baya barin Wannan nafila, yana kula da ita fiye da sauran nafiloli

SAHIHUL BUKHARI: 1169

Kamar yadda mukayi bayani a rubutun da ya gabata cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

Rakao’i guda biyu na Alfijir (Raka’ata Alfajr) sunfi duniya da abinda ke cikin ta alheri

SAHIHU MUSLIM: 725

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: