Hukuncin Hada Salloli biyu don lalurar ruwan sama ko matsanancin laka ko sanyi

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Tambaya: Shin ya halatta a haɗa salloli biyu ayisu lokaci ɗaya don lalurar ruwan sama ko sanyi ko laka ko zubar dusan ƙanƙara da makamantansu na lalurori?

Amsa: Ya Halatta a haɗa salloli biyu a lokaci ɗaya don lalurar ruwan Sama, ko sanyi mai tsanani, ko zubar dusan ƙanƙara da sauran lalurori Wanda Maluma suka ambata, kamar lalurar tafiya wanda yakeyin ƙasaru zai iya haɗa Sallah, haka nan mara lafiya da rarrabe Sallah yake masa wuya……

Dalili:

Sa’id bin Jubair ya rawaito daga Ibn Abbas Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya haɗa tsaƙanin Sallar Azahar da La’asar, da kuma Magrib da Isha’i a Madina ba’a cikin tsoro ko ruwan sama, sai Sa’id bin Jubair yace wa Ibn Abbas meyasa ya aikata haka? Sai yace Domin kada ya takura wa Al’ummar sa.

Sahihu Muslim: 705

Wannan yake nuna cewa ya Halatta a haɗa tsaƙanin salloli biyu sabida uzuri Wanda shari’ah ta yarda da shi kamar Uzurin ruwan sama da makamantansa.

Amma baya halatta a haɗa salloli biyu ba tare da uzuri ba.

Wannan haɗa Sallah da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi, yayi ne don ya nuna halaccin haɗa Salloli idan akwai Uzuri, domin sau ɗaya aka Rawaito Annabi ya haɗa Sallah sabida haka wannan bazai zama hujja ba na cewa a rinƙa haɗa Sallah ko babu uzuri. Wannan shine taƙaitaccen abinda Maluma suka faɗa game da wannan Mas’ala.

Ga maison neman ƙarin bayani zai iya duba Littafin “Kash-shaful ƙanna” na Al-Buhuti (2/5) Babban malami ne Mazhabar Hanbaliyya, ya kawo yanayi da ake haɗa salloli acikin Babin haɗa salloli guda biyu.

Leave a Reply

Latest updates
Categories