Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 5: Mutuwar Abdulmuddalib

Shekara kafin Hijira: 46

Shekarar Miladiyya: 577


Kamar yadda mukayi bayani a baya. Bayan rasuwar mahaifiyar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Wanda ya ɗauki nauyin kula dashi shine kakansa Abdulmuddalib. Ya kasance yana son annabi sosai kuma yana bashi kulawa.

Bayan da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yakai shekaru takwas a rayuwarsa Allah yayi wa kakansa Abdulmuddalib cikawa. Lokacin da mutuwa tazo wa Abdulmuddalib sai yayi wa ɗansa Abu Ɗalib wasiyya da cewa ya kula da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Da kuma biya masa duk buƙatunsa.

Ibnu Sa’id da Ibnu Asakir sun rawaito cewa:

Lokacin da Abdulmuddalib ya rasu, sai Abu ɗalib ya ɗauki Manzon Allah, yaci gaba da kula dashi. Ya kasance yana tare da manzon Allah. Ya kasance yana son Manzon Allah irin son da baya yi wa ƴaƴan cikinsa, ya kasance baya bacci har sai in Manzon Allah na kusa dashi. Ya kasance yana keɓance shi da abinci. Iyalan Abu ɗalib sun kasance idan sunci abinci su kaɗai ba tare da Manzon Allah ba basu ƙoshi. Amma idan suka ci tare da Manzon Allah sai su ƙoshi. Sun kasance idan zasu ci abinci sai Abu ɗalib yace su jira har sai Manzon Allah ya iso. Idan Manzon Allah yazo sai suci abincin su ƙoshi har subar saura. Amma idan ba tare dashi sukaci ba to basu ƙoshi. Idan kuma ya kasance Nono zasu sha toh Annabi shi yake fara sha kafin sai su sha su ƙoshi. Amma in suka sha su ƙadai basu ƙoshi. Abu ɗalib yakan ce wa Annabi haƙiƙa kana da Albarka.


Wannan Tarihi ina tsaƙuroshi ne daga Mausu’ah ta Tarihi ta “dorar.net” domin karantawa cikin harshen larabci Danna nan. Domin yin gyara Danna nan

Donate to support Us. May Allah reward You with Jannah
Account Number: 3077875210
Account Name: Mukhtar Muhammad
Bank: First Bank Nigeria
You can also Click Here to Donate Online

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You may use these HTML tags and attributes: <a href="" title=""> <abbr title=""> <acronym title=""> <b> <blockquote cite=""> <cite> <code> <del datetime=""> <em> <i> <q cite=""> <s> <strike> <strong>

%d bloggers like this: