Tarihin Annabi Fitowa ta 9: Farkon Sauƙar wahayi da Annabcin Annabi Sallallahu alaihi wasallam

Shekara kafin Hijira: 13

Shekarar Miladiyya: 610


Farkon Abinda ya fara gani na Alamun Annabta shine Mafarki na gaskiya, ya kasance duk abinda ya gani yayin bacci yana aukuwa idonsa biyu, sannan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance a lokacin yana keɓance kansa a ƙogon Hirá yana Bautar Allah, ya kasance yana wannan bautan ne akan Addinin Annabi Ibrahim Alaihissalam.

Yana cikin wannan harkar bautan sai wata rana Mala’ika Jibrilu Alaihissalam yazo masa da faɗin Allah:

“Kayi Karatu”

Suratul Alaq Ayah 1- 6

ya dawo gida ya baiwa Matarsa Sayyada Khadija Labarin Abinda ya faru, ita kuma taje ta baiwa dan’uwanta Waraqah Bin naufal labari, ya gaskata Wannan labari da ta bashi, yace ai wannan Mala’ika Jibrilu ne wanda yaje wa Annabi Musa.

daga nan sai wahayi ya yanke zuwa wani lokaci, sai Jibrilu Alaihissalam ya sake dawo wa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama sai Annabi yaji tsoronsa, ya dawo zuwa ga iyalansa yace “Ku lulluɓeni, Ku lulluɓeni” sai Allah Maɗaukakin sarki ya sauƙar da faɗin sa:

Ya wanda ya Lulluɓa da mayafi

Suratul Mudaththir: Ayah 1-5

Wannan shine farkon Ayah da Allah ya umarci Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da yaje ya kira Mutane.

Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 8: Hukuncin Annabi kan dora Hajarul Aswad a mazauninsa

Shekara kafin hijira: 18

Shekarar Miladiyya: 605


An samu tsaɓani tsaƙanin ƙabilu a lokacin sake gina ɗakin ƙa’abah kan wanene zai ɗaura Baƙin dutse(Hajarul Aswad) a mazauninsa! Ƙabilar Quraish wacce itace annabi ya fito daga cikinta suka nemi cewa su zasu ɗaura wannan dutse a mazauninsa, wasu daga cikin ƙabilu suma suka ce sune zasu ɗaura.

Read More…

Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 7: Auren Manzon Allah da Khadijah da kuma tafiyar sa zuwa sham karo na biyu

Shekara kafin Hijira: 28

Shekarar Miladiyya: 595


An samu tsaɓani wurin tabbatar da shekarun Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma na Khadijah Radiyallahu Anha lokacin aurensu.

wasu sukace Manzon Allah ya aure ta lokacin yana da shekaru ashirin da biyar, wasu kuma suka ce ashirin da bakwai, wasu kuma suka ce talatin. Wasu sun faɗa wasu shekarun ba wannan ba.

Read More…

Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 6: Tafiyar Annabi da baffansa zuwa Sham

Shekara kafin hijira: 42


Shekarar Miladiyya: 581


Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yakai shekara goma sha biyu. Baffansa Abu Ɗalib wanda shine yake ɗaukan nauyin annabi kaman yanda mukayi bayani a baya. Ya ɗauki annabi Sallallahu alaihi Wasallama zuwa Ƙasar Sham acikin tawagar ƴan kasuwa. Lokacin da suka isa Busra sai tawagar ta yada zango domin hutu sai manzon Allah da baffansa suka wuce kusa da wani fada(Malamin Kirista) na Kiristoci.

Read More…

Tarihin Annabi Fitowa ta 2: Tsaga Ƙirjin Manzon Allah da Mala’ika Jibrilu yayi Lokacin yana yaro

Tsaga Ƙirjin Manzon Allah da Mala’ika Jibrilu yayi Lokacin yana yaro:

Kafin Hijira: 49

Shekarar Miladiyya: 575


An rawaito hadisi daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace:

Mala’ika Jibrilu yazo wurin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama lokacin yana wasa da yara, ya kamashi ya kwantar dashi, sai ya tsaga ƙirjinsa, sai ya ciro zuciyarsa, sai ya cire wani gudan jini daga zuciyar, sai yace wannan shine rabon da shaiɗan yake dashi a jikinka, bayan haka sai ya wanke zuciyar A cikin wani kwano na Gwal da ruwan zamzam, sannan sai ya haɗe zuciyar ya kuma maidashi mazauninsa, bayan da wa’innan yara da suke wasa tare da Manzon Allah suka ga haka sai suka garzaya zuwa ga mai rainonsa(Halimatu-ssa’adiyyah). Suka bata labarin cewa An kashe Manzon Allah, sai suka zo wurin Mazon Allah suka sameshi yanayinsa ya canza alaman cewa akwai wani abu da ya sameshi.

– Muslim 268


Read More…

سيرة النبي

Tarihin Annabi Fitowa ta 1: Haihuwar Annabi

Download

Haihuwar Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama).

Kafin Hijira: 53

Shekarar Miladiyya: 571


Maluman Tarihi sun samu tsaɓani kan takamammen rana da kuma wata da aka haifi Manzon tsira(Sallallahu alaihi Wasallama). Sai dai kuma sun samu haɗuwa kan cewa an haifi Manzon Allah ne Ranan Litini a shekarar giwaye.

Ibnul Qayyim yana cewa:

babu tsaɓani kan cewa an haifi Manzon Allah ne a cikin Garin Makkah, sannan kuma an haifeshi ne a shekarar giwaye.

-Zadul Ma’ad Fi Hadyi khairil ibaad 1/76.


An rawaito daga Ibn Abbas Allah ya ƙara Masa yarda yana cewa:

An haifi Manzon Allah ne A shekarar Giwaye.


Read More…