Hajjin Bankwana(Hajjatul Wada’i)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Shekarar Hijira: 10

Shekarar Miladiyya: 631


Ankira wannan Hajjin da Hajjin Bankwana Sabida Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi bankwana da Mutane a wannan Hajjin. kuma bai sake yin wani Hajji ba bayan sa. Sannan ana kiran wannan Hajjin da wasu sunaye kamar Haka:

  • Hajjin Musulunci(Hajjul Islam): Domin Annabi baiyi wani Hajji ba daga Madina sai ita.
  • Hajjin Isarwa(Hajjul balag): Domin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya isar wa Mutane Shari’ar Allah A baki da kuma aikace. Ya zamto babu wani abu na Ginshiƙan Addinin Musulunci face Annabi yayi bayaninsu.

Lokacin da Annabi Yayi Wa mutane bayanin Hukunce Hukuncen Hajji, yayi Musu sharhinsa Sai Allah ya sauƙar da Wannan Aya mai girma ta cikin Suratul Ma’idah.

A yau ne na cika muku Addinin ku, na kuma cika muku Ni’ima ta, kuma na yarje muku Musulunci ya zamo muku Addini

Suratul Ma’idah – 3

Wannan Ayah ta sauƙa ne a filin Arafa.

A Wannan Hajji Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi Bayanin Shari’ar Musulunci da Haramcin Zubar da Jinin Musulmi ba tare da Haƙƙi ba. Yake cewa:

Lallai Jinanenku, da Dukiyoyinku, Da Mutuncinku Haramun ne akanku.

Sahihul Bukhari: 4406 Muslim: 1679

Baya Halatta ku kashe kawunanku, Ko ku ɗebi dukiyar Junanku ba tare da Yarda ba, ko ku keta Alfarmar junanku ta Yin zina, Liwaɗi ko ƙazafi da sauransu. Duka wannan Haramun ne.

Lokacin da Annabi Yayi shelar zuwa wannan Hajji Mutane da yawa suka zo Madina domin tafiya tare da Manzon Allah, domin yin aiki irin na Manzon Allah.

A wannan Hajji ne Annabi Yayi Huɗubarsa mai Matuƙar Mahimmanci wanda zamuyi sharhin ta nan gaba Insha’Allah.

Leave a Reply

Latest updates
Categories