Daga cikin ladduban cin abinci

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Kamar yadda kowa ya sani ne addinin musulunci addini ne wanda yazo da komai, babu wani abu na lamarin wannan addini face Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yayi bayaninsu. Yau zamuyi bayani ne kan wasu ladduba na cin abinci.

  • Lashe hannu da kuma kwano bayan kammala cin abinci: wannan yana daga cikin ladubba da mutane sukayi sake dashi matuƙa. An rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana umarni da mutum ya lashe hanunsa da kuma kwanonsa bayan kammala cin abinci, kamar yadda Muslim ya rawaito. Annabi yake cewa bakusan a ina ne albarkan abincin yake ba. Muslim 2033. Sai dai ya kamata a guje wa lashe hannu yayin cin abinci sai an kammala musamman indai mutum yana cin abincin tare da mutane ne, domin hakan zaisa masu cin abincin tare su kyamace abincin.
  • Idan abinci ya faɗi a ɗauka a karkaɗe aci: shima wannan yana daga cikin ladubban cin abinci, idan abinda kake ci ya faɗi ka ɗauka ka karkaɗeshi sannan kaci. Sai dai inya zamto irin wanda baza a iya rabashi da ƙasa bane ko kuma abinda ya shafeshi. Misali kaman kana cin nama sai ya faɗi, sai ka ɗauke shi ka karkaɗe kaci kayanka. Annabi yana cewa: idan loman ɗayanku ya faɗi a ƙasa, ya ɗauke ta ya kawar da abinda ya shafe ta na datti, sannan yaci. Muslim 2033

Wani bincike na Kimiyya da aka gudanar ya nuna fa’ida ta lashe hannu bayan cin abinci, inda binciken ya nuna cewa a lokacin da mutum ya lashe hannunsa bayan cin abinci, toh hannun yana fitar da wani sinadari da yake sauƙaƙa narkewan abinci a ciki. Wannan mun kawoshi ne domin ƙara nuna fa’idar umarnin Manzon Allah, amma bashine dalili da zaisa mu lashe hannunmu bayan cin abinci ba, muna lashewa ne sabida annabi yayi umarni da muyi haka.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories