Hukuncin Carbi

Tambaya: menene Hukuncin Amfani da carbi wurin yin zikiri ko Salatin Annabi da makamantansu?

Amsa: Wasu daga cikin maluma sun tafi kan halaccin Amfani da carbi, duk da cewa suma sun tabbatar da cewa yin amfani da hanu shi yafi falala. Wasu Maluman kuma sun tafi kan cewa Amfani da carbi bid’ah ne.

Sheikhul Islam ibn Taimiyya Allah yayi masa rahama yace:

Sau da dama ana samun masu amfani da carbi kaga ɗaya daga cikinsu ya rataya sallaya a kafaɗarsa, sannan ya riƙe carbi a hannun sa, sai ya sanya wannan abinda yayin a matsayin Alama ne na Addini. Abune sananne a addini cewa Annabi da Sahabbai basu kasance suna aikata wannan abu suna bayyana shi a matsayin wani alama na Addini ba, Sun kasance suna yin tasbihi suna kuma lissafa wa ne da Hannun su. Kamar yadda aka rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. Yace “ku lissafa su(Ma’ana Tasbihi da sauran zikirori) da Yatsunku, domin Za’a tambaye su ranar tashin Alƙiyama, kuma zasuyi magana”.

Majmu’u Fatawa: 22/187

Yaci gaba da cewa:

Game da amfani da carbi wurin ƙirge akwai wa’inda suka ce makruhi ne, akwai wa’inda kuma sukayi rangwame kan haka. Amma babu wanda yace yin tasbihi da carbi yafi yi da hannu.

Majmu’u Fatawa: 22/187

Sannan yace:

Amfani da carbi yana sa riya ya shiga cikin aikin mutum, kuma wannan Riya ne da abinda ba’a shar’anta ba, wanda yafi muni fiye da riya cikin abinda aka shar’anta.

Majmu’u Fatawa: 22/187

Sheikh Muhammad Nasirud-din Albani Allah yayi masa rahama ciki ta’aliƙinsa da yayi kan rashin ingancin hadisin da yazo kan ƙwaɗaitar wa game da amfani da carbi wannan hadisi: نعم المذكّر السبحة

Yace:

Yace ma’anar wannan hadisi a wurina ɓatacce ne saboda abubuwa kaman haka:

Na farko: Lallai carbi bid’ah ce bata da asali a zamanin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, an same ta ne bayan shi. Ta yaya zai yiwu Annabi ya kawaɗaitar da Sahabban sa kan abinda basu san shi ba.

Dalili kan abinda na faɗa shine abinda Ibnu waddah ya rawaito acikin Littafin “Albida’i wannahyu anha” daga Salt bin Bahram yace:

Ibnu Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya wuce wasu mata suna tasbihi da carbi sai ya yanka carbin ya yar.

Sannan wata rana ya wuce wani mutum yana amfani ƙananun duwatsu wurin tasbihi sai ya buge shi da ƙafan shi yace masa:

Kunyi rige, kun aikata Bid’ah bisa zalunci. Sannan kun fi Sahabban Annabi ilimi.

Na biyu: Yin amfani da carɓi tsaɓanin Shiryarwar Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ne.

Abdullahi bin Amru yace:

Naga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana ƙirga Tasbihi da Hannunsa na dama.

Silsilatul Ahadisi-Sahiha 1/110

Abin Lura: Carbi bashi da Asali a Addinin Musulunci. Ya samo asali ne daga Addinin Budha kaman yadda wasu Maluman sukayi bayani. A Zamanin Annabi ana amfani ne da hanu wurin Yin Tasbihi da zikirori. Kuma inda sunaso suyi amfani da carbi da zasu iya yi. Amma basu yi ba. Yin amfani da Carbi tsaɓanin Sunnar Annabi ne. Sannan kuma yana janyo riya saboda duk wanda aka ganshi da carbi za’a ce wannan mai yawan Zikiri ne. Sannan yin tasbihi da carbi yana sanya gafala yayin yin zikiri. Sau da dama zaka samu masu amfani da carbi zaka samu suna tasbihi amma zuƙatansu na wani wuri. Amma wanda yake amfani da hannunsa wurin yin tasbihi sau da dama zaka ga yana halarto abinda yake faɗa saboda ƙirgawa da yake yi. Saboda Haka abinda ya dace Musulmi yayi shine ya tsaya inda Annabi da Sahabbansa suka tsaya. Domin dukkan Alheri yana cikin bin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: