Hukuncin wanda yayi Sallah ba zuwa ga Alqibla ba A mantuwa

·

·

,

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Tambaya: Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?

Amsa: yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce, sabida Allah yace “Ka juya da fuskarka zuwa ga masallaci Tsararre” (Baqara 144). Da umarnin da annabi(Sallallahu alaihi wasallam) yayi yace “Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.
Maluman sun tafi akan cewa wanda
yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta ba,  
an tambayi maluman ‘Lajnatudda’imah’ kan hukuncin matafiyi da ya isa gari, yayi sallah ba zuwa ga alqibla ba, kuma bai tambaya ba, baiyi bincike ba, suka bada amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alqiblar, (Lajnatudda’imah Majmu’ah ta biyu 5/294).
Da haka, ya wajaba akan wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alqibla sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai suna akan bazai sake ba. kuma hakan shine daidai……. Allahu A’alam.


Click Here To Contact Us For Any Enquiry.

Leave a Reply

Latest updates
Categories