SUNNAH CE KADA A CI KOME A SAFIYAR IDIN LAYYA HAR SAI AN DAWO DAGA IDI TUKUN

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoYana daga cikin abin da yake Sunnah a ranar idin Layya kada a ci abinci sai bayan an gama sallar idi tukun an dawo. Sannan shi kuma mai abin layya zai yi buda-bakin ne da hantar layyarsa; saboda dalili kamar haka:-
Imamut Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 546, da Imam Ahmad Hadithi na 22,984, da Imam Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1426, da Imamud Daaraqudniy Hadithi na 1715, da Imam Ibnu Hibban Hadithi na 2812, da Imam Haakim Hadithi na 1088, da Imamul Baihaqiy cikin Sunan Hadithi na 6380, da Ma’arifatus Sunan Hadithi na 1912 da Isnadi Sahihi daga Sahabi Buraidah Bin Susaib Allah Ya kara masa yarda ya ce:
((كان النبي صلى الله عليه وسلم لا يخرج يوم الفطر حتى يطعم، ولا يطعم يوم الأضحى حتى يصلي)).
Read More…

MA'ANAR SALAFIYYAH

By: Dr. Ibrahim Jalo JalingoMa’anar Salafiyyah shi ne: bin hanyar magabata; watau Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina wajen girmama Annabi mai tsira da amincin Allah, da barin maganar kowa a duk lokacin da ta yi karo da maganarsa, da nuna fashi da damuwa a duk lokacin da aka ga wani ya yi watsi da maganar; Saboda wannan matsayi lalle shi ne matsayin Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina. Ga misalai kadan na irin yadda Sahabbai suke girmama maganar Annabi, suke bin maganarsa sau-da-kafa, suke kuma nuna fushinsu a kan duk wani da ya ki bin maganarsa ya koma yana bin maganar waninsa:- 1. Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3093, da Muslim Hadithi na 1759 cewa babban Sahabi Sayyidina Abubakar As-Siddiq ya ce:-
((لست تاركا شيئا كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعمل به الا عملت به فاني اخشى ان تركت شيئا من أمره ان أزيغ)).
Read More…

IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR:

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo


Idan idi ya kasance a ranar Juma’a to babu wajibcin sallar Juma’a a ranar; wannan hukuncin ne za a iya fahimta in aka yi kyakkyawan nazari cikin hadithai biyar da suka zo cikin wannan babin, hadithan kuwa su ne kamar haka:- (1) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,070 da Imam Ibnu Majah hadithi na 1,326 da isnadi sahihi daga Iyas Dan Abii Ramlah ya ce:-
((شهدت معاوية بن ابي سفيان وهو يسال زيد بن أرقم قال: أشهدت مع رسول الله صلى الله عليه وسلم عيدين اجتمعا في يوم؟ قال: نعم. قال: فكيف صنع؟ قال: صلى العيد ثم رخص في الجمعة، فقال: من شاء ان يصلي، فليصل))
. Ma’ana: ((Na halarci Mu’awiyah Dan Abii Sufyaan yana tambayar Zaid Dan Arqam ya ce: Ko ka halarci Idi biyun da suka hadu a rana guda tare da Manzon Allah? Sai ya ce: Na’am. Sai ya ce: to yaya ya yi? Sai ya ce: Ya yi sallar Idin sannan ya rangwanta yin sallar juma’a, ya ce: Wanda ya so yin sallar sai ya yi sallar)). (2) Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1,329 da isnadi sahihi daga Sahabi Abdullahi Dan Umar ya ce:-
Read More…

MUTUMIN DA KE DA MATA 4 SANNAN YA YI WA DAYANSU YANKAKKEN SAKI KO ZAI HALATTA YA AURI WATA MATAR KAFIN IDDAR WANNAN TA CIKA?(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

1. Babu sabani tsakanin Malamai cewa: ba ya halatta ga namiji ya hada Ya da Kanwa karkashin aurensa a lokaci guda. Haka nan ba ya halatta gare shi ya daura wa mace ta biyar aure koda kuwa akwai wacce ya saka saki na kome matukar dai ba ta gama iddarta ba. Wannan mas’ala babu sabani a cikinta tsakanin Malaman Sunnah; saboda dalilai da yawa daga cikinsu akwai: Fadar Allah cikin surar Nisaa’i aya ta 23 ((Kuma kada ku hada tsakanin Ya da Kanwa saifa abin da ya riga ya wuce)). Da kuma wasu hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, daga cikinsu akwai hadithi na 2243 da Imam Abu Dawud ya ruwaito, da hadithi na 1952 da Imam Ibnu Majah ya rueaito, da hadithi na 4631 da Imam Ahmad ya ruwaito, da hadithi na 4156 da Imam Ibnu Hibban ya ruwaito dukkansu da isnadi sahihi cewa Sahabi Wahb Al-Asadiy ya musulunta alhalin yana da mata 8 sai Annabi mai tsira daRead More…

Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuceshi

Mutum ne yazo sallan gawa sai ya tarar da liman ya riga yayi kabbara biyu ko fiye da haka meye hukuncinsa? zai yi kabbara ya fara daga karatun fatiha ne ko kuma zai fara daga  inda limamin yake ne sannan daga karshe ya rama kabbarorin ko kuma bazai rama su ba?
Amsa:
idan mutum wasu kabbarori suka wuceshi daga cikin kabbarorin sallan gawa toh in yazo zaiyi kabbara ne sannan ya fara karanta fatiha, zaiyi lura da cewa wannan kabbarar itace farkon kabbararsa, sannan in limami ya kammala sallan shikuma zai tsaya ya kammala kabbarorin da suka wuceshi da sauri, in har ba’a dauke gawar ba, amma in aka dauke gawar to kawai zaiyi kabbarorin da suka wuce masa ne ajere ba tare da bata lokaci ba ko yin
addu’oi bayansu, dalilin da yasa malamai sukace wanda wasu kabbarori suka wuceshi na sallan gawa zai cikesu shine umumin fadin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam),
Read More…