001 Fiqhu: Ruwa da rabe rabensa

Bismillahirrahmanirrahim.

Ruwa ya rabu kashi uku gasu kamar haka:

•Ruwa mai tsarƙi mai tsarƙaƙewa: Shine ruwa wanda yake a asalinsa, wanda bai cakuɗu da wani abu ba, najasa ko ba najasa ba. Kamar ruwan Kogi, Rijiya, Sama, kududdifi da makamantansu. Duka irin wa’innan ruwa masu tsarƙi ne, ana iya shansu, sannan kuma ana iya yin aikin Ibada dasu.

Ruwa mai tsarƙi wanda baya tsarƙaƙewa: Shine ruwa wanda ya cakuɗu da abu mai tsarƙi. Kamar ruwan da ya cakuɗu da Siga, ko gari. To wannan ruwa Mai Tsarki ne a karan kansa amma kuma baya tsarkake wa, ma’ana za’a iya shan ruwan, ko kuma ayi aikin gida dashi, amma baza’ayi aiki na ibada dashi ba, kamar alwala ko wankan janaba da makamantansu.

Read More…