Yawaita yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati a dare da ranar Juma’a

Yana daga cikin ibada mai falala yiwa Annabi Salati, musamman a daren juma’a da kuma ranar juma’a, Annabi ya bada Labarin cewa ana bujuro mishi da duk salati da akeyi masa. Shin kana so a bujuro da salatinka kaɗan?

Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

إنَّ مِن أفضَلِ أيَّامِكم يومَ الجُمُعةِ؛ فأكثِروا عليَّ مِن الصَّلاةِ فيه؛ فإنَّ صَلاتَكم معروضةٌ عليَّ

سنن أبي داود: ١٥٣١
Read More…

Ranar Aashura da kuma falalar azumi acikinsa

Ranar Aashura: shine ranar goma ga watan Al-muharram, kuma rana ne da akeso musulmi ya azumceshi sabida falaloli dake cikinsa, sannan kuma anaso wanda zaiyi azumin ranar Aashura ya azumci ranar tara .

Falalar Azumin Ranar Aashura: Abu Qatada Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yace :

Azumin ranar Aashura tana kankare zunuban shekarar da ta gabata.

– Muslim 2746-2747


Kuma Manzon Allah yana fifita azumin wannan rana ta Aashura akan waninsa, kamar yadda aka rawaito daga Ibn Abbas Allah ya ƙara masa yarda

– Bukhari 2006


Tunatarwa: Ba’a rawaito daga Annabi ko Magabata na gari cewa wannan Rana ta Aashura ranace ta nuna baƙin ciki ko kuma yin wasu bukukuwa ba, Abinda aka Rawaito shine yin azumi a wannan Rana, sai mu gujewa yin duk wasu abubuwa da basu da asali wanda bazasu jawo mana wani amfani ba, sai dai abinda zai cutar damu, a duniyanmu da kuma Addinin mu.

Anaso Mai yin Azumin Aashura ya azumci ranar tara

Anaso mai yin Azumin Aashura ya azumci ranar tara ga wata wato rana daya kafin Aashura. Domin lokacin da annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya azumci ranar Goma ga watan Al-muharram kuma yayi umarni da azumtarshi sai aka bashi Labari cewa wannan rana ne da Yahudu da Nasara suke girmama wa, sai yace toh in shekara ya zagayo in Allah ya yarda zamu azumci ranar tara ga wata.Kuwa shekarar bata kewayo ba Allah ya karɓi Manzon Allah.

– Muslim 1134Read More…