Ramadaniyyat: 1444 (11) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Ramadaniyyat: 1444 (11)

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (11)

Ci gaba…..

  1. Yayin da Sheikhul Islam yake tsare a kuruku, su kuma mabiyansa suna can cikin damuwa. Wata ƙila ma damuwar mutanen Sham ce ta sa sarakunan Masar suka fara tunanin fito da Ibnu Taimiyya. Su ma malamai suka fara gindaya sharuɗɗan da suka tabbatar da cewa ba zai taɓa yarda da su ba.
  2. Bayan wancan yunƙuri ya ci tura, sai can bayan wani lokaci suka yi wani tunani sabo, watau shi ne su ɗauko ‘yan’uwan nan nasa biyu, domin su yi magana da su amma da sunansa. Sai suka kawo su kotu. A nan ne tattaunawa ta ɓarke tsakanin ɗan’uwan Ibnu Taimiyya, watau Sharafuddin da Alƙalin Malikiyya Zainuddin Ibnu Makhluf. Ɗan’uwan Sheikhul Islam bai yi wata-wata ba ya ƙure shi da hujja. Ibnu Kasir yana ba da labari ya ce: “Sharafundin ya ƙure Alƙalin Malikiyya da hujja da dalili da ilimi. Ya bayyana kurakurensa a kan wasu batutuwa da ya yi ta cika baki a kansu. Sun tattauna a kan mas’alar Al’ardh da Al-Kalam, da mas’alar saukar Allah (SWT)”.
  3. Bayan wannan tattaunawar ne Sheikhul Islam ya samu fitowa daga gidan yari, a ranar 23 ga watan Rabi’ul Auwal, shekara ta 707, bayan ya kwashe shekara biyu da wata goma sha takwas a tsare.

Ibnu Taimiyya Ya Yafe Wa Maƙiyansa:

50 Fitowar Ibnu Taimiyya ke da wuya daga wurin da yake a tsare, sai ya nufi wuraren yake gabatar da darasi, ya ci gaba da yi wa jama’a karatu a masallatai, yana gabatar da huɗubar juma’a, har kusan tsawon wata shida. Ya samu masoya da mabiya da yawa a Masar kamar yadda yake da su a Sham.

  1. Babban abin da Ibnu Taimiyya ya yi bayan fitowarsa wanda ya ja hankalin mutane da dama, shi ne yadda ya shelanta yafiyarsa ga duk waɗanda suka cutar da shi har suka yi sanadiyya zamansa a kurukuku na watanni masu yawa. Ibnu Taimiyya ya rubuta hakan a wata wasiƙa da ya aika wa mutanen Dimashƙa, inda yake cewa: “Kun riga kun sani – Allah ya yarda da ku- ba zan so a cutar da wani musulmi da kowane irin abu ba, ballanta kuma in so irin hakan ga almajiranmu; ko a sarari ko a ɓoye. Kuma ba wanda nake zargi ko tuhuma. Ina matuƙar ganin girmansu da jin ƙaunarsu fiye da ma yadda nake ji a da, kowanne daidai da matsayinsa. Dukkansu dai ba su wuce ɗaya daga cikin mutane uku ba: Ko mai ijtihadi ko mai kusukure ko mai laifi. Na farko yana da lada kuma abin a gode masa ne; na biyu kuma tare da ladan ijtihadinsa, abin yi wa afuwa ne; na uku kuma, Allah ya gafarta mana, mu da shi da sauran muminai… Ba na son wani ya yi ramuwar gayya a kan wani da aka same shi da laifin yi mini ƙage ko zalunta ta ko cutar da ni. Na yafe wa duk wani musulmi da ya yi mini laifi. Ina so wa dukkan Musulmai alheri. Ina so wa duk wani mumin alheri kamar yadda nake so wa kaina. Duk waɗanda suka zalunce ni ko suka yi mini ƙage, ni a ta ɓangarena, na yafe musu”. [Al-Fatawa, juz. 28, Sh. 52, Ibnu Abdil Hadi, Al-Uƙudud Durriyya, sh. 278].

Za mu ci gaba insha Allah……

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories