Ramadaniyyat: 1444 (27) Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (27)

Ci gaba…..

Siffofin Ibnu Taimiyya:

  1. Allah (SWT) ya yi wa Ibnu Taimiyya wasu siffofi na musamman waɗanda su ne suka haɗu suka yi shi a matsayin babban malami da ya cika ya tumbatasa a zamaninsa, wanda kowa ya riƙa ba da labarin tarin sani da Allah ya ba shi. Waɗannan siffofi su ne kamar haka:
  2. Na ɗaya, ƙarfin hadda. Wannan shi ne harsashin farko na bunƙasar ilimin kowane malami. Gwargwadon yadda Allah ya hore wa malami ƙarfin hadda da kiyeye abin da ya karanta, gwargwadon yadda matsayinsa zai kasance a cikin tsarekunsa malamai. Ibnu Taimiyya ya siffantu da wannan siffa ta ƙarfin hadda, tun daga farkon tasowarsa yana yaro har zuwa rasuwarsa.
  3. Na biyu, zurfin tunani. Duk wata mas’ala da Ibnu Taimiyya zai ɗauko, to zai tsaya ya yi nazarin ta nazari mai zurfi. Yakan yi nazarin ayoyi da hadisai da mas’alolin da suka danganci hankali da ƙiyasi, yakan tsaya tsai, ya yi amafani da lafiyayyen hankali da miƙaƙƙen tunani ya auna tsakaninsu. Don haka Ibnu Taimiyya ba wai kawai hadda ce da shi ba, a’a ya haɗa da zurfin tunani da gano abubuwa yadda suke.
  4. Na uku, saurin fahimta. A cikin sauƙi yake gano abubuwa ya fahimce su ba tare da ya sha wahala ba. Duk sa’adda yake tattauna wa da mutum, cikin ƙanƙanin lokaci yake kai shi bango saboda yawan haddarsa da kuma saurin fahimtarsa. A dalilin wannan siffa ce ta Ibnu Taimiyya ya sa abokan hamayyarsa suke shayin su yi gaba-da-gaba da shi. Wanda kuwa bai san shi ba, har ya kuskura ya gaba-da-gaba da shi, to zai kwashi kashinsa a hannu, zai kuma yi da-na-sanin artabu da shi.
  5. Na huɗu, tunani mai ‘yanci. Wannan siffar da Ibnu Taimiyya ya siffanta da ita, ita ce ta mayar da shi malami na musamman a cikin malaman da suka yi zamani ɗaya da shi. Ɗaya daga cikin almajiransa yana bayanin wannan siffa ta Ibnu Taimiyya inda yake cewa: “Duk sanda gaskiya ta bayyana a gare shi, to yana cije ta da kyau da fiƙoƙinsa. Wallahi ban taɓa ganin mutum mai girmama Manzon Allah (SAW) da tsananin kwaɗayin yi masa biyayya da taimakon abin da ya zo da shi, kamar Ibnu Taimiyya ba. Idan ya ci karo da wani hadisi a kan wata mas’ala wanda babu wani hadisin da ya shafe hukuncinsa, to zai yi aiki da shi, ba ruwansa da duk wata magana ta wani mahluki da ta saɓa masa. Kuma ba ya tsoron wani sarki ko wani mai mulki ko wani makami. Ba zai taɓa barin Alƙur’ani da sunna don wani ba. Mutum ne da yake riƙe da igiyar Allah mai ƙarfi”.
  6. Na biyar, Ikhlasi a wajen neman gaskiya, da tsarkaka daga ƙazantar son zuciya da wata manufa ta duniya. Ikhlasi shi ne yake jefa haske a zuciyar mumini, yake sanya shi ya fahimci abubuwa yadda suke.

Za mu ci gaba in sha Allah…

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories