Ramadaniyyat: 1444 (28) Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (28)

Ci gaba…..

Siffofin Ibnu Taimiyya [2]

  1. Ikhlasin Ibnu Taimiyya ya bayyana a wurare huɗu:

a) Yayin da yake fuskantar malamai da iya abin da ya fahimta, babu abin da yake gabansa sai neman yardar Allah, ko mutane za su ji daɗi ko ba za su ji daɗi ba.

b) Gwagwarmayar da ya yi don Allah kaɗai, wadda ta kai har sai da ya ɗauki takobi ya fafata da abokan gaba. Ya yi matuƙar jure wahalhalu don bayyana ra’ayinsa a koyaushe. Ya sha ɗauri daga maƙiyansa har ma daga masoyansa.

c) Daga cikin abin da yake nuna Ibnu Taimiyya ba ya da son zuciya ko neman duniya, shi ne yadda muka ga ya yi afuwa ga malaman da suka ƙuntata wa rayuwarsa, suka sa aka ɗaure shi ba tare da ya yi musu wani laifi ba. Amma lokacin da ya samu damar ɗaukar fansa a hannunsa, sai ga shi ya yi musu afuwa gaba ɗaya, ya kuma iya afuwa ga waɗanda suka ƙuntata masa a ƙarshen rayuwarsa har ta kai ya rasu a kurkuku.

d) Yayin da ya guje wa duk wani matsayi ko shugabanci, ya nisanci duk wani ƙaleƙalen duniya. Bai karɓi wani muƙami na hukuma ba, bai yi faɗa da wani a kan neman matsayi ba. Ya yarda ya ci gaba da zamansa malami mai wa’azi, mai bincike, bai shiga takara da kowa a kan wani muƙami ba. Ya zamanto koyaushe yana tare Allah, ba ya neman ceton kowa sai na Allah, kuma Allah ya tsirar da shi. Zahabi yana cewa: “Sau tari maƙiyansa sun haɗa kai sun shirya masa makirci, to amma sai Allah ya kuɓutar da shi. Shi mutum ne mai yawan ambaton Allah. Mai yawan neman taimakonsa, mai ƙarfin dogaro ga Allah, mai dakiya (marar tsoro). Yana da wurudai da zikirai da kullum yake yin su”.

  1. Na shida, Jarumta, tare da haƙuri da juriya. Ibnu Taimiyya ya nuna jarumta a fagen yaƙi da lokacin da ya jiɓinci al’amarin tafiyar da ƙasa, da wajen yaƙi da ɓarna bayan hare-haren Tatar suka haifar da rashin hukuma a garin Dimashƙa. Hakanan a tsawon rayuwarsa ya nuna jarumta lokacin da shi kaɗai yake tunkarar abokan husumarsa. Ya rungumi sunna, ya bayyana ta ko da kuwa ta saɓa wa abin da mutanen gari suka saba da shi, wanda yin haka ya jawo masa gamuwa da jarrabawa iri-iri. A kuma wannan lakaci ne siffar haƙuri da juriya suka sake bayyana a tare da shi. Haƙuri wanda bai san ƙosawa ba, da juriya wadda ba ta san sarewa ba. Ya rabu da mutane tsawon shekara biyu amma bai yi rauni ko laushi ba. Ya ci gaba da gudanar da aikinsa babu ƙaƙƙautawa. Tare da waɗannan siffofi kuma Allah ya yi masa kwarjini da yake cika zuciyar abokin hamayyarsa da tsoro.

Za mu ci gaba in sha Allah…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories