Ramadaniyyat: 1444 (18) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (18)

Ci gaba…..

Dawowar Ibnu Taimiyya Ƙasar Sham:

  1. Ibnu Taimiyya ya sauke nauyin da ke kansa na isar da ilimi da wa’azi. Ya sha fama wajen bayyana gaskiya, ya jure wahalhalu daban-daban. Yanzu ya kamata ƙwarai ya koma garinsa a cikin danginsa da ‘yan’uwansa, ya ci gaba da rayuwa a lungunan da ya taso har ya girma a cikinsu. To amma sai ga shi duk waɗannan abubuwa ba su ne suka sa shi ya koma ƙasar yarintarsa ba. Ba abin da ya mayar da ƙasarsa sai jihadi. Domin a watan Shawwal na shekarar 712 Sarki Nasir Muhammad ɗan ƙalwun ya tanadi wata gagarumar runduna, domin tunkarar mayaƙan Tatar, saboda ya ji labarin sun nufo Sham don su tayar da hankulan mutane su kuma tabka ɓarna a bayan ƙasa. To a nan ne Sarki ya buƙaci Ibnu Taimiyya da ya kasance tare da shi, don haka Sheikh ba yi ƙasa a gwiwa ba wajen shiga cikin wannan rundunar mayaƙa. Sai ga shi ya dawo garin Dimashƙa yana ɗauke da takobi bayan ya zama dattijo wanda ya haura shekara hamsin, alhali a baya ma ya saɓe takobinsa yana matashi ɗan shekara arba’in.
  2. Ibnu Taimiyya ya iso Dimashƙa a farkon watan Zulƙi’ida na shekarar 712, to amma sai Allah ya ɗauke wa muminai yaƙi. Rundunar Tatar suka ranta a na kare babu mai waiwayen bayansa daga cikinsu.
  3. Daga nan Ibnu Taimiyya ya ci gaba da zama a Sham bai sake fita daga cikinta ba. Ibnu Kasir ya ba da labarin rayuwarsa a Sham a daidai wannan lokacin inda yake cewa: “Sannan Sheikh bayan isowarsa Sham, sai ya mayar da hankalinsa baki ɗaya kan sha’anin ilimi da yaɗa shi da rubuta littattafai da yi wa mutane fatawa baki-da-baki ko kuma a dogayen rubuce-rubuce. Da kuma ƙoƙarin binciken hukunce-hukuncen shari’a; yana yin fatawa da fahimtarsa gwargwadon ijitihadinsa; wani lokaci ya tafi daidai da mazhabobi huɗu; wani lokacin kuma ya saɓa musu, ko ya saɓa wa abin da ya fi shahara a cikinsu. Yana da zaɓaɓɓun ra’ayoyinsa masu dama waɗanda ya assasa su gwargwadon ijitihadinsa, ya kuma kafa musu dalilai daga Alƙur’ani da Sunna da maganganun sahabbai da sauran magabata”.

Za mu ci gaba insha Allah…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories