Ramadaniyyat: 1444 (9) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat: 1444 (9)

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (9)

Ci gaba…..

Ibnu Taimiyya Ya Fara gamuwa Da Jarrabawa:

  1. Malamai sun fara kai ƙarar Ibnu Taimiyya gaban mahukunta a Masar, suna ta faɗin miyagun maganganu a kansa. Daga cikin mahukuntan nan akwai waɗanda ba su gama sanin wane ne Ibnu Taimiyya ba, saboda kasancewarsa a ƙasar Sham yake da zama ba a Masar ba, amma kuma a nan a Masar ne ake shirya masa ƙulle-ƙulle a ɓoye; ake yaɗa cewa ya kauce wa madaidaiciyar hanya, yana kuma sukar aƙidar Ash’ariyya wadda suke ɗaukar ta da ƙima sosai. Ta fuska guda kuma, Sarki Nasir, wanda shi ne mai sarautar da yake ganin girman Ibnu Taimiyya, ƙarfin mulkinsa ya fara rauni, har ya fara rasa matsayinsa na mai faɗa a ji; kwamandojinsa sun fara yi masa bore da bijire wa umarninsa.
  2. Gwargwadon yadda matsayin Sarki Nasir yake ƙara rauni, gwargwadon haka mugun tanadin da ake yi wa Ibnu Taimiyya yake ƙara haɓaka. An shirya majalisai daban-daban waɗanda suka ƙunshi maƙiyan Ibnu Taimiyya da mahassadansa da masu jin haushinsa, don su yi nazari a kan al’amarinsa, su kuma samar da hanyar da za a bi wajen cutar da shi ko a hana shi ci gaba da karantarwarsa. Daga ƙarshe aka cimma matsaya a kan cewa, a kirawo shi zuwa Masar. Aka rubuta masa takardar gayyata mai cike da yaudara, a ciki ana faɗa masa cewa: “Mun ji labarin an haɗa wa Ibnu Taimiyya majilisin tattaunawa da shi. Kuma an yi majalisai da shi, an kuma tabbatar da cewa yana kan hanyar magaba (watau a aƙida). To mu ma a nan muna son mu wanke shi daga duk wata tuhuma da ake yi masa”. Sai kuma aka sake tura wata takardar ana umartar sa da ya yi maza-maza ya taho Masar da zarar takardar nan ta je hannunsa.
  3. Ibnu Taimiyya mutum ne mai tunkarar duk wani abu da ya taso masa, ba ya guje wa wani abu ko ya ji tsoron sa, don haka ya ƙuduri aniyar tafiya zuwa Masar, amma Magajin garin Dimashƙa, da ya fahimci makircin da ake ƙoƙarin ƙulla wa Ibnu Taimiyya sai ya hana shi tafiya, amma Ibnu Taimiyya ya dage sai ya tafi, domin yana ganin akwai maslaha a tafiyar tasa, saboda ko ba komai yana da buƙatar ya je Masar don ya amfanar da jama’a, ya bayyana musu fahimtarsa, ko da hakan zai cutur da shi.

Jarrabawa Ta Farko:

  1. Sheikh ya isa Masar a shekara ta 705 bayan hijira. Lokacin da Ibnu Taimiyya yake yada zango a hanya yana gabatar da darussa ga jama’a, su kuma abokan hamayyarsa suna can a Masar suna shirye-shiryen yadda za su ƙulla masa makirci idan ya iso. Yana iso wa Masar aka shirya masa Majalisi a Fada. Manyan alƙalai da manyan ƙasa suka hallara. Ibnu Taimiyya ya nemi a ba shi dama ya yi magana, amma sai aka hana shi magana kwata-kwata, domin ana tsoron ƙarfin hujjarsa da kaifin bayaninsa. Sai kawai suka fara jefa masa tuhumce-tuhumce. Mai gabatar da ƙara a kansa kuma shi ne Alƙalin Malikiyya Zainuddin Ibnu Makhluf. Sai ya tuhume shi da cewe yana cewa: “Allah yana saman Al-Arshi a bisa haƙiƙa, kuma Allah yana magana da harafi da sauti”. Sai Ibnu Taimiyya ya fara hamdala ga Allah da yabonsa, domin ba da amsar tuhumar da ake masa, sai kawai aka ce masa: “Ka ba da amsa kawai, ba huɗuba za ka yi mana ba”. To daga nan ya fahimci ana so ne a hukunta shi, ba wai ana so a tattauna da shi ba ne, sai ya yi tambaya: “Wane ne alƙalin da zai yi mani shari’a?”Sai aka ce masa: “Alƙalin Malikiyya”, wato Ibn Makhluf. Sai Sheikh ya ce masa: “Ta yaya za ka zama alƙali a kaina alhalin kai ne abokin rigimata”. Daga nan Alƙali ya fusata sosai, hankalinsa ya tashi, ya yi umarni a je a tsare Ibnu Taimiyya a kurkuku. Ibnu Taimiyya ya tafi kurkuku tare da ‘yan’uwansa biyu: Sharafuddin da Zainuddin waɗanda suka rako shi Masar.

Za mu ci gaba insha Allah….

Wannan Shafi na Bukatar Gudumawarku domin gudanar da ayyukansa na yau da kullum, Zaku iya taimaka wa da duk abinda kuke dashi komin kankantan sa ta wannan account.

Account Number: 8247620882
Bank: MONIEPOINT MFB
Name: The Light Of Islam

Ko Kuma ku danna nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: