Ramadaniyyat: 1444 (12) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (12)

Ci gaba…..

Wasiƙar Ibnu Taimiyya Zuwa Ga Mahaifiyarsa:

  1. Ibnu Taimiyya yana fitowa daga kurkuku, sai mahaifiyarsa ba buƙaci ta yi ido biyu da shi, shi kuma a daidai wannan lokacin yana ganin aikinsa a Masar bai ƙare ba, domin yana son ya sauke wajibin da yake kansa a wannan gari, kamar yadda ya sauke shi a Sham, don haka ne sai ya rubuta wa mahaifiyarsa wasiƙa yana lallashin ta da kwantar mata da hankali. A cikin wasiƙar yake cewa: “Daga Ahmad Ibnu Taimiyya zawa ga mahaifiya mai arzuki. Allah ya faranta mata ranta da ni’imominsa, ya kwararo mata gwaggwaɓan karamcinsa, ya sanya ta daga cikin bayinsa masu yi masa hidima… Muna yi wa Allah godiya a bisa ni’imominsa, muna kuma roƙon sa ya ƙara mana daga falalarsa. Duk sa’adda ni’imar Allah ta zo, to tana ƙara haɓaka ne da ƙaruwa, ga kuma wasu ɗimbin ni’imomin da sun fi ƙarfin lissafi. Kuna sane da cewa, mun ci gaba da zama a wannan ƙasa domin wasu al’amura na larura waɗanda idan muka kuskura muka yi watsi da su, to sai su lalata mana al’amarin addininmu da na rayuwarmu. Wallahi ba muna so muka zaɓi mu yi nesa da ku ba. Da a ce tsuntsaye za su iya ɗaukar mu, da tuni ma mun zo gare ku. Sai da matafiyi izurinsa yana tare da shi. Kuma muna rantsuwa da Allah, da a ce ku ma kun san abin da yake ɓoye, to da zaɓinku ba zai wuce irin namu ba. Abin da muke roƙo kawai shi ne ku yawaita yi mana addu’a ta alheri. Allah shi ne ya sani, mu ba mu sani ba, shi ne mai iko, mu ba mu da wani iko, shi ne masanin gaibu…. Matafiyi idan ya yi tafiya yakan ji tsoron dukiyarsa ta salwanta, sai ya buƙaci ya ci gaba da zama a garin da ya je har sai ya gama tattara dukiyarsa. Al’amarin da muke ciki ya fi ƙarfin bayani. Babu wata dabara ko wani ƙarfi sai tare da Allah. Muna sallama a gare ku da sauran mutanen gida: manya da ƙanana da abokan arzuki; ɗaya bayan ɗaya. Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa”. [Al-Uƙudud-Durriyya, sh. 273-274, da Al-Fatawa, juz. 28, sh. 48-50].

Jarrabawa Ta Biyu:

  1. Duk da daɗewar da Ibnu Taimiyya ya yi a Masar, kullum yana niyyar koma wa gida Sham. Sai dai kuma yana nasa Allah ma yana nasa. Don haka Allah ya rubuta masa dogon zama fiye da yadda yake tsammani, sai kuma Allah ya sake jefa shi cikin wata sabuwar jarraba.
  2. Wannan jarrabar a wannan karon ba ta fito ta ɓangaren fuƙaha’u ko malaman Ilmul Kalam ba. A’a ta fito ne ta ɓangaren Sufaye waɗanda suke da babban matsayi a Masar. Tun can da jimawa Sarki Salahuddin Al-Ayyubi ya gina musu Zawiya, sannan Sarki Nasir Al-ƙalawun da ya zo, shi ma ya sake gina musu wata a shekara ta 723.
  3. Sannan wasu daga cikin mabiya ɗarikar Sufanci a Masar suna da aƙidar ‘Wahdatul Wujudi’ wadda Ibnu Arabi ya yi rajin tallatawa a cikin wasu rubuce-rubucensa da waƙe-waƙensa. Daga cikin waɗanda suka tasirantu da shi akwai mawaƙin nan ɗan ƙasar Masar mai suna Umar ibnul Faridh, wanda ya rasu shekara ta 632 bayan hijira. Wasu cikin sufayen Masar suna riya cewa, idan sun kai wani yanayi na tarbiyya da tsaftace zuciya, to za su haɗe da Zati Maɗaukakiya, daga nan kuma sun fi ƙarfin bautar Allah ko aiki da Shari’a. To Ibnu Taimiyya sam bai gamsu da wannan sheɗanar ba. Hakanan sa’adda yake Sham bai yarda da wani dabo ko rufa-ido na ‘yan ɗariƙar Rufa’iyya ba. Don haka ya zare kansakalin yaƙar waɗannan aƙidu miyagu. To a dalilin yaƙi da su ne dole sai ya yaƙi ra’ayoyin Muhyiddin Ibnu Arabi, saboda haka ya shiga yaƙar su ka’in da na’in, ba tsoro ba ja da baya.

Za mu ci gaba insha Allah……

Wannan Shafi na Bukatar Gudumawarku domin gudanar da ayyukansa na yau da kullum, Zaku iya taimaka wa da duk abinda kuke dashi komin kankantan sa ta wannan account.

Account Number: 8247620882
Bank: MONIEPOINT MFB
Name: The Light Of Islam

Ko Kuma ku danna nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: