Ramadaniyyat: 1444 (17) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (17)

Ci gaba…..

  1. A wannan karon Ibnu Taimiyya ya dawo Al-Ƙahira ne da niyya zama a cikinta. Don haka ya aika Dimashƙa don a kawo masa wasu daga cikin littattafansa. Ya mai da hankalinsa gaba ɗaya wajen karantarwa da wa’azi da fatawa. Ba wani malami da ya sake fito wa fili ya soke shi. Har su kansu sufaye ba su iya fito wa sarari don su soki maganganunsa ba, ba kuma saboda sun yarda da abin da yake faɗa ne ba, ko don suna jin tsoron Allah, a’a sai don tsoron mai martaba Sarki.
  2. Wannan ya sa abokan hamayyarsa daga cikin Fuƙaha’u da Sufaye suka koma suna shirya masa ƙullalliya ta ƙarƙashin ƙasa a ɓoye. Suka fara zuga gama-garin mutane a kansa. Sai dai kash sun makaro, domin kuwa tuni Ibnu Taimiyya ya sami ɗimbin magoya baya fiya da nasu, saboda ƙarfin hujjarsa da iya bayaninsa. Abubuwa biyu sun faru:
  3. Na farko, a ranar huɗu ga watan Rajab na shekarar 711 wani gungun mutane sun haɗu da shi yana shi kaɗai, suka shiga cin mutuncinsa, har ma suka kai ga ɗaga hannayensu suka doke shi. Kafin ka ce kobo, sai ga jama’ar unguwar da yake da zama, watau ‘Husainiyya’ sun yi cincirindo suna ƙoƙarin ɗaukar masa fansa daga waɗannan gungun jama’ar da suka doke shi. Suka nace wa Ibnu Taimiyya da magiya a kan ya ba su izini su je su ɗaukar masa fansa, amma sai ya ce musu: “Haƙƙin nan, ko dai ya zama nawa ne; ko kuma naku ne; ko kuma na Allah ne. To idan haƙƙin nawa ne, to ni na yafe musu. Idan kuma naku ne, to idan ba za ku ji maganata ba, to ku je ku yi duk abin da kuka ga dama. Idan kuma haƙƙin Allah, to Allah da kansa zai nemi haƙƙinsa insha Allah”.
  4. Abu na biyu, A wannan wata ne dai, wani malami ya faɗi wasu miyagun maganganu na cin mutunci a kan Ibnu Taimiyya, sai kuma daga baya ya dawo ya ba shi haƙuri. Yana yiwu wa, ya ba shi haƙuri ne don yan tsaron fushin mai martaba Sariki, saboda matsayin da Ibnu Taimiyya yake da shi a wurinsa. Sai dai shi Sheikh ya yafe masa, yana mai faɗar cewa: “Ba zan taɓa ramuwar gayya don kaina ba”.
  5. A wannan zaman da Sheikhul Islam ya yi a Al-Ƙahira ya kasance mai ba wa Sarki shawara a kan wasu al’amura da ya hango. Daga cikin irin shawarwarin da ya ba shi: An riƙa samun yawan karɓar cin hanci wajen ba da wasu muƙamai na hukuma da wasu al’amura, amma Ibnu Taimiyya ya matsa lamba wajen nuna wa Sarki Nasir illar wannan abu, har sai da ya yarda ya rubuta wa sarakunan da ke ƙarƙashinsa takarda da kakkausan harshe yana faɗa musu cewa: “Kada a sake ɗora wani a kan wani muƙami don ya ba da rashawa ko wasu kuɗaɗe, domin yin haka zai haifar da shugabantar da waɗanda ba su dace ba”. Hakanan al’amarin ƙisasi ya riƙa gudana taci-barkatai babu tsari, har al’amarin ya kai mutane suna yawan ɗaukar doka a hannunsu. A nan ma Sarki ya matsa lamba, lalle a riƙa bibiyar al’amura da kyau. Sannan ya nemi a riƙa saurin zartar da ƙisasi idan ya tabbata, kuma kada a kuskura a zartar wa wani ƙisasi ba a ƙarƙashin shari’a ba.

Za mu ci gaba insha Allah…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories