Ramadaniyyat: 1444 (15) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (15)

Ci gaba…..

Ibnu Taimiyya Ya Sake Karawa Da Sufaye

  1. Wannan shi ne lokacin da aka sami karawa ta haƙiƙa tsakanin Ibnu Taimiyya da Sufaye, bayan Sarki Nasir bn Ƙalawun ya sauka daga kan kujerar sarauta da raɗin kansa, kuma Sarki Al-Muzaffar Bibaras Al-Jashankir ya ɗare kujerar mulki. Wannan sabon Sarki kuwa ba shi da wani malami da yake girmamawa yake kuma yi masa makauniyar biyayya kamar Sheikh Nasrul Manbiji, wani shehi sufi mai matsanancin ra’ayin riƙau a kan sha’anin Ibnu Arabi. A nan aka samu karon batta mai tsanani da Ibnu Taimiyya, saboda ƙarfin faɗa a ji da Al-Manbiji yake da shi da kuma fada a wurin sabon Sarki. Sannan kuma ga shi ana yi wa Ibnu Taimiyya kallon ɗaya daga cikin magoya bayan Sarki Nasir mai barin gado.
  2. Sarki Al-Jashankir da Al-Manbiji sun yi ta ƙulle-ƙullen yadda za su ɓullo wa Ibnu Taimiyya, sai suka ga matakin da ya kamata su ɗauka shi ne su kori Ibnu Taimiyya zuwa Al-Iskandariyya, tunda ya riga ya tara magoya baya a garin Al-Ƙahira, kuma ga shi an samu wasu daga cikin Fuƙaha’u suna goyon bayansa. Amma a can Al-Iskandariyya ba shi da wani mataimaki ko mai goyon bayansa, don haka suna ma fatan wani ɗan zafin kai ya yi masa kisan gilla kowa ya huta.
  3. Yayin da su Al-Manbiji suke tsaka da ƙulle-ƙullen makircinsu, tuni labarin Ibnu Taimiyya da iliminsa da martabarsa sun isa garin Iskandariyya. Ilimi fitila ce wadda haskenta ba inda ba zai je ba matuƙar babu wani abu da ya kare shi.
  4. Ibnu Taimiyya ya isa Al-Iskandariyya a daren ƙarshe na watan Safar, shakara ta 709. Isarsa garin ke da wuya sai ya fara gudanar da darussa da wa’azuzzuka. Ya yi wata bakwai a haka, har zuwa lokacin da Sarki Nasir ya dawo kan karagar mulkinsa bayan ƙaurace masa da ya yi na wucingadi.
  5. A daidai wannan lokacin ne Ibnu Taimiyya ya sake haɗuwa da wasu abokan hamayya waɗanda su ma dole ya tunkare su da iliminsa. A nan garin Al-Iskandariyya ne ya haɗu da wata ƙungiyar sufaye da ake kira da ‘Sab’iniyya’ wato waɗanda ake danganta su da wani malami sufi mai suna Ibn Sab’in wanda ya ɓullo da hanyar gauraya sufanci da ilimin falsafa, wato shi sufi ne kuma malamin falsafa.
  6. Ibnu Taimiyya ya ɗauki gabarin wa’azi da gargaɗi a kan wannan ƙungiya, bai tsagaita musu ba har sai da ya yi fata-fata da su, ya karya musu kadari. Mabiyansu suka riƙa tururuwa zuwa ga Ibnu Taimiyya suna bayyana tubansu, har shi da kansa shugaban ƙungiyar tasu ya zo ya bayyana tubansa a gaban Ibnu Taimiyya. Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya rubuta cikakken littafi babba don fallasa miyagun aƙidu da ra’ayoyin Ibnu Sab’in; littafin da ake kira da suna ‘As-Sab’iniyya’, ko kuma ‘Bugyatul Murtad’. Allah (SWT) ya cika zukatan al’ummar garin Al-Iskandariyya da ƙaunar Ibnu Taimiyya da ganin girmansa, shi kuma Nasrul Manbiji da jama’arsa suka cika da baƙin ciki da ƙasƙanci da fargaba marar yankewa. Allahu Akbar! Allah mai yin yadda ya ga dama..

Za mu ci gaba insha Allah….

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories