Ramadaniyyat: 1444 (8) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Ramadaniyyat: 1444 (8)

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (8)

Ci gaba…..

Ibnu Taimiyya Ya Fara gamuwa Da Jarrabawa:

  1. Matsayin Sheikhul Islam Ibnu Taimayya ya ƙaru bayan da ya fito daga fagen neman ilimi ya tsunduma fagen aikin da iliminsa, domin ya ba wa Musulunci da Musulmi kariya daga ɓarnar maɓarnata. Martabarsa ta ƙaru a idon Sarki Nasiruddin ƙalawun wanda shi ne kwamandan yaƙin ƙarshe da aka gwabza da ‘yan ta’addar Tatar aka kawo ƙarshensu a faɗin yankin ƙasashen Larabawa.
  2. Al’amarin Ibnu Taimiyya a idon mahukunta ya ƙara buwaya, ya kai matakin da sai an nemi shawararsa kafin a naɗa wani malami a kan wani muƙami na addini. Shi ne ya ba da shawarar naɗa Kamaluddin As-Sharisi a matsayin babban shehin Darul-Hadis Al-Kamiliyya bayan rasuwar Taƙiyuddin Ibn Daƙiƙil Id. Ya kai matsayin da babu wani limamin juma’a da za a naɗa, ko wani mai wa’azi, ko wani shugaban makarantar addini sai an ji ta bakinsa. Abin ma bai tsaya iya haka ba, lamarinsa a hukumance ya kai ga zai iya horar da masu laifi idan sun yi wa al’umma laifi.
  3. An ba da labari cewa, wata rana an zo da wani daga cikin shehunan Baɗiniyya wanda aka fi sani da suna ‘Hasshashun’, wato ƙungiyar da suka halatta shan wiwi domin aikata ta’addanci, waɗanda su ne suka addabi Hukuma a zamanin Sarki Salahuddin Al-Ayyubi da sarakunan da suka biyo bayansa na Daular Ayyubiyya, bayan waɗannan sarakuna sun sami nasarar karya lagon kiristoci a yaƙe-yaƙen da suka yi da su. Sai Ibnu Taimiyya ya ga wannan Shehi ya bar gashin kansa buzu-buzu, ya bar faratan yatsunsa zaƙo-zaƙo, ya tara gashin baki buyu-buyu, sai ya sa aka saisaye masa gashin kansa, aka kuma rage masa gashin baki, aka yanke masa faratansa. Ya nemi shi da ya tuba daga zagin sahabbai da muminai da yake yi, ya kuma daina shan kayan maye kamar wiwi, ya kuma daina aikata haramtattun ayyuka. Sannan ya sa shi ya rubuta alƙawari a kan ba zai ƙara fassara wa mutane mafarki ba, wanda da shi ne yake jan hankalin jama’a.
  4. Wannan matsayi da Ibnu Taimiyya ya samu a wurin Hukuma ya ƙara jawo masa hushin malamai wanɗanda da ma can suna cike da shi, saboda fatawoyinsa da ra’ayoyinsa da suka saɓa da nasu. Sannan a gefe guda kuma mabiya sufanci su ma sun cika da haushinsa, saboda yana sukan Muhyiddin Ibnu Arabi a kan ra’ayinsa na ‘Wahdatul Wujud’ da ‘Hululi’ wanda su kuma waɗannan sufaye suna girmama shi a matsayin ɗaya daga cikin shugabanninsu na Tasawwuf. Bugu da ƙari wasu daga cikin waɗannan malamai suna ganin sun girme shi a shekaru, wasu ma malamansa ne. Don haka wannan lamari na Ibnu Taimiyya ya riƙa ci musu towo a ƙwarya, su da almajiransu da sauran jama’ar da suke ganin girmansu, suke kyautata musu zato.

Za mu ci gaba insha Allah…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates