Sharrin dake kunshe da fina finan Tarihin Musulunci

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh

Bismillahir-Rahmanir-Raheem.

A yau zan ja hankalinmu ne kan wata musiba da take yawo acikin mu, wannan musiba kuwa itace fina finan tarihin musulunci.

Karantar tarihi abu ne mai matuƙar amfani ga kowata Al’ummah, domin akwai abubuwa da yawa wadda zamu amfana dasu, zamu amfana da hanyoyin da magabatanmu sukayi amfani dashi wurin samun Nasara, da kuma gwagwarmaya da sukayi wurin kafa wannan Addini, hakanan zamu amfana da kurakurai da sukayi domin muma mu kauce mata.

Sabida haka ne Maluman Musulunci sukayi rubuce rubuce masu yawa kan tarihi, suka fara tun daga zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama har zuwa yau basu daina ba, duk abinda ya faru suna rubuta shi domin na baya suzo su karanta su amfana.

Read More…

Hukuncin Magana yayin Hudubar Juma’a

Tambaya: Shin ya halatta mutum yayi magana yayin Hudubar Liman?

Amsa: Baya halatta mutum yayi magana yayin hudubar liman.

Dalili: Allah madaukakin sarki yace:

Idan aka karanta Al-Qur’ani Ku saurara, sannan kuyi shiru

Suratul-Aaraf: 204

Imam Ahmad yace:

Maluma da yawa sun tafi kan cewa wannan ayah ta sauka ne kan Sallah da kuma Khudbah

Fathul Bari: 5/499

Dalili na Biyu: Abu Huraira ya rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi wasallama yace:

Idan kace wa Abokinka ranar Juma’a kayi shiru alhali liman yana khudbah toh kayi lagawu(Yasasshen zance)

Bukhari: 934
Muslim: 851

Wannan Hadisi yana nuna haramcin magana a yayin khudubar Liman, sabida in ya zamto Cewa da zakayi wa Abokin zamanka yayi shiru laifi ne duk da cewa kana Umarni ne da kyakkyawa ashe magana wanda ba wannan ba shi yafi kasance wa Haramun.

Abin Lura: Baya halatta Wanda yaje masallacin Juma’a yayi magana yayin hudubar Liman, koda ko yaga wani yana magana ba zai hanashi a wannan lokaci ba, sai dai ya bari in Liman ya kammala huduba.

Hukuncin Jiyarwa a sallah (Ladanci)

Tambaya: an tambayi Sheikh Bin Baaz Rahimahullahu game da ladanci sai yace

Amsa: idan har mutane suna jin sautin liman babu bukatar sai an jiyar, amma idan akwai wasu wanda basu ji, kaman wa’inda suke waje ko suke karshen sahu toh Mustahabbi ne a jiyar. Annabi Sallallahu alaihi wasallama yayi sallah wata rana a lokacin rashin lafiyarsa a lokacin muryarsa na da rauni sai Abubakr Yana daga murya yana jiyarwa.

Abin lura: Dalilin da yasa aka jiyar a lokacin Annabi shine rashin lafiyarsa, kuma muryarsa bata kaiwa yacce ta dace, shiyasa bayansa ba’a samu sahabbansa sunci gaba da jiyar wa ba.

Toh a wannan zamani namu da akwai amsa kuwwa mune yafi dace wa kada mu jiyar sabida kowa zai iya jin muryar liman har da wanda yake waje.

Allah yasa mudace.

Reference: Shafin Sheikh Bin Baaz

Hukuncin yin Bismillah lokacin alwala

Tambaya: Shin yin Bismillah lokacin yin alwala wajibi ne? Idan Mutum baiyi ba alwalarsa babu?

Amsa: Ansamu tsabani tsakanin Maluma game da wajabcin yin Bismillah yayin alwala. Mafi yawan Malamai sun tafi kan cewa ba wajibi bane, Sunnah ne, sabida haka idan mutum baiyi ba don mantuwa ko da gangan alwalarsa tayi, sai dai yin Bismillar itace tafi dace wa, kuma bai dace mutum ya bar yinta ba da gangan. Wasu Maluman kuma sun tafi akan cewa yin Bismillah wajibi ne.

Read More…

Hukuncin zane Ko tattoo a Musulunci

Tambaya: Meye hukuncin zane ko tattoo a musulunci?

Amsa: yin zane ko tattoo haramun ne A Musulunci ga namiji da mace.

Dalili: Abdullahi bin Mas’ud ya rawaito Annabi Sallallahu alihi wasallama yana cewa:

Allah ya tsine wa mai yin zane da wanda ake yi mata

Bukhari: 5948

Wannan hadisi ya nuna cewa haramun ne Mutum musulmi yayi zane ko tatto a jikinsa. Domin duka hukuncinsu daya, namiji ko mace.

Yaya hukuncin wanda akayi masa yana yaro?

Wannan Allah bazai kama shi da laifi ba, domin bashi ya sanya ayi masa ba, laifin yana kan wanda yasa ayi masa inhar ya san cewa Annabi ya hana kuma yayi.

Allah shine mafi sani.

Fara yin Kasaru kafin tafiya

Tambaya: Shin mutum zai iya fara Yin kasaru tun daga gida kafin ya bar garin da yake?

Amsa: baya halatta ga mutum ya fara sallar kasaru har sai ya bar garin da yake koda bai isa inda yake nufi ba, idan har tazarar da yake tsakanin garin da ya bari zuwa inda yake a yanzu zai bashi daman yin kasaru.

Dalili: Allah ya bada wannan rangwame ne ga matafiyi, kuma mutum baza’a kirashi matafiyi ba har sai ya bar gidansa ya kama tafiya, kuma wannan bai kama tafiya ba. Haka nan Allah yace:

Idan kunyi tafiya acikin Kasa, babu laifi a gareku ku rage Sallah

Suratun-Nisa’i: Aya 101

Anan Allah cewa yayi idan kukayi tafiya. Hakanne yasa mutum bazai fara yin kasaru ba har sai ya fara tafiya.

Allah shine mafi sani

Hukincin Sallah da takalmi

Tambaya: Mene hukuncin yin Sallah da takalmi?

Amsa: Ya Halatta ayi Sallah da takalmi idan har an tabbar da cewa tana da tsarki, babu najasa a jikinta.

Dalili: an rawaito daga Abi Maslama sa’ad bin yazid Al-Azdi yace na tambayi Anas Bin Malik Allah ya kara masa yarda, shin Annabi Ya kasance yana Sallah da takalminsa a kafansa? Sai yace Eh.

Bukhari: 386
Muslim: 555

Abin lura: idan ya zamto mutum Masallaci zai shiga yayi sallah, Masallaci da akayi shimfida toh zai cire takalminsa ne yayi sallah babu takalmi, sabida kada Ya shigar da datti masallaci, amma in ya zamto a hanya yake, ko a wuri wanda babu shimfida toh zaiyi sallar sa ne da takalminsa.

Haka nan kuma mutum kafin yayi sallar sai ya lura da kasan takalminsa ya tabbatar babu najasa, in akwai sai ya kawar da wanman najasar sa’anan Yayi sallah.

Allah yasa mudace.