Hukuncin ajiye kare a gida domin gadi

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Fatawa

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Shari’ar Musulunci ta Haramta wa Musulmi ajiye kare ba tare da wani dalili ba, kamar mutum ya rike shi a matsayin abokin zama, yana wasa dashi, ko yana fita dashi yawo, kamar yadda wa’inda ba Musulmai ba sukeyi.

Duk wanda ya riki kare batare da wani uzuri ba, kamar Gadi, ko Farauta to ko wani rana zara rinka rage masa ladansa.

An rawaito daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda yace, Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yace:

Wanda ya riki kare ba karen gadin gona ba, ko farauta, ko gadin Dabbobi, Za’a rinka rage masa ladansa kowani rana.

Bukhari: 5163 Muslim: 1574

Wannan shine Hukuncin Rikar kare, baya halatta sai dai idan an riki karen ne sabida wa’innan abubuwa uku da muka lissafa.

  • Gadin gona
  • Gadin Dabbobi
  • Farauta

Shin ya Halatta Mutum ya ajiye kare a gida domin gadi?

Imamun-Nawawy Allah yayi masa Rahama yace:

An samu tsabani game da rikar kare badun wa’innan abubuwa uku da aka ambata ba, amma abinda yafi inganci shine ya Halatta Qiyasi akan wa’innan Abubuwa uku da aka ambata.

Sharhu Muslim 10/236

Sheikh Bin Uthaymeen Allah yayi masa rahama yace:(Ma’anar maganarsa)

Abisa haka, gida wanda yake cikin gari bashi da bukatar a sanya kare a cikinsa, duk wanda ya riki kare ya sanya a gidansa bisa wannan hali ya aikata haramun, kuma za’a rinka rage ladansa a kullum. amma in ya zamto gidansa na wajen gari ne babu kowa a kusa to babu laifi ya riki kare domin kare gidansa da wa’inda suke cikinsa.

Majmu’u Fatawa: 4/246

Abin lura anan shine:

Idan mutum ya zamto gidansa barayi suna damunsa ko kuma yana tsoron Barayi zasu shiga gidan acikin gari gidan yake ko a wajen gari, kuma bashi da wata hanya da zai tsare gidan sai ta amfani da kare to anan babu laifi, sabida tsare gida da lafiyar masu gida yafi tsare gona da dabbobi, amma Shari’a ta bada dama a riki kare wurin tsare dabbobi da gona, to hakan yake nuna rikarsa wurin tsare gida idan akwai bukatar hakan shi yafi karfi.

Idan mutum ya zamto bashi da wata hanya ta tsare gidansa sai ta hanyar sanya kare toh sai yayi kokari ya sanya karen nesa da cikin gidansa, kuma kada ya rinka yawo dashi, ko ya rinka rungumarsa da makamantansa, kuma da zarar ya samu Aminci ko wani hanya ta tsare gidan nasa to yayi kokari ya rabu da wannan karen. hakan shi yafi dacewa.

Allah byasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories