Hadisi: Kalma da mutum zai furta ka iya jefa mutum cikin wuta

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

An rawaito daga abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace;

Lallai bawa zai rinƙa furta wata kalima ba tare da yayi binciken abinda ta ƙunsa ba, Zai nitse cikin wutan Jahannama a ta dalilin wannan Kalima Fiye da nisa tsaƙanin Maɓullan rana da mafaɗan ta.

Sahihul Bukhari: 6478

Wannan Hadisi yana nuna mana hatsarin harshe da wajabcin kame harshe. Ba komi bane mutum zai rinƙa furta wa. Domin wani abinda mutum zai rinƙa furta wa yana ƙunshe da tsaɓa wa Allah wanda hakan zai kai mutum zuwa ga halaka.

Shiyasa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci musulmi Wanda yayi Imani da Allah da ranar ƙarshe da ya faɗi alheri ko yayi shiru.

Mutum ya kame ga barin shiga abinda babu ruwan shi, sannan duk abinda zai rinƙa furtawa yasan me ya ƙunsa. Kada yaji ana faɗan abu shima ya faɗa.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories