Hanyar karban Addu’a

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Addu’a tana da Mahimmanci, sabida Mahimmancin ta ne yasa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Lalle Addu’a Shine ibada

Abu Dawud: 1479 Tirmidhi: 2969

Sai dai Addu’a yana Ladduba da Kuma Hanyoyi da ya kamata mutum yabi domin samu a Amsa Addu’ar sa. Yana daga cikin Wannan Hanyoyi Abinda aka Rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ummu Sulaim Allah ya ƙada mata yarda taje Wurin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi tace: Ya Manzon Allah ka Sanar dani wata Kalma wacce zan rinƙa roƙon Allah da ita, Sai Annabi yace: Kiyi Tasbihi(Subhanallah) wa Allah sai goma, Kiyi Tahmidi(Alhamdulillah) sau goma, kiyi Kabbara (Allahu Akbar) sau goma, sannan sai ƙi roƙi buƙatar ki, Allah zaice na aikata na aikata

Imamu Ahmad: 11797

Wannan Hadisi yana koyar damu Wannan hanya ta roƙon Allah maɗaukakin sarki, Shine kafin mutum yayi Addu’ar sai yace Subhanallah sau goma, Alhamdulillah sau goma, Allahu Akbar sau goma, sannan sai ya roƙi abinda yakeso.

akwai wata riwaya wanda Annasa’i ya kawo da tace wa Annabi ka sanar dani wata kalma da zan roƙi Allah da ita acikin Sallah ta. Sabida haka ne wasu Maluman suke ga Hadisin na Magana ne akan Addu’a bayan tahiya ko bayan Sallame wa.

Sabida haka idan mutum yayi shi bayan tahiya, ko bayan sallame wa daga Sallah duka yana da kyau.

Allah maɗaukakin sarki ya amsa mana Buƙatun mu na Alheri.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories