Ku zaba wa yayanku sunaye masu kyawu

Yan daga cikin Haƙƙoƙin Yara akan iyayensu, su zaɓa musu suna mai kyawu, Domin shi suna Yana nuni akan wanda ake kiransa dashi, Shiyasa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yake so wa Musulmi sunansa ya zamto mai kyawu, baya ƙunshe da mummunan Ma’ana.

Mafi Soyuwan sunaye Awurin Allah

Abdullahi bin Umar ya rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Lallai mafi soyuwan sunayenku a wurin Allah sune Abdullahi da Abdurrahman

Sahihu Muslim: 2132

Abdullahi: Ma’anar sa Bawan Allah shine suna na farko da Allah yafi so, ya ƙunshi kaɗaita Allah da bauta.

Abdurrahman: Ma’anar sa Bawan Mai Rahama, Arrahman yana daga cikin sunayen Allah kyawawa. Wannan shine suna na biyu da yafi soyuwa a wurin Allah.

Duk wani Suna da ya ƙunshi Ubudiyya wa Allah maɗaukakin sarki suna ne mai kyawu, Kuma Allah yana son shi. Bayan wa’innan sai sunayen Annabawa da sunayen bayi na ƙwarai.

Yana da kyau mutum ya guje wa ƙaƙale wurin sanya wa ƴaƴansa suna, Da guje wa sanya sunar da ba’a san ma’anar sa ba.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: