Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.
Bismillahir-Rahmanir-Raheem.
Tambaya: Shin ya halatta ayi yanka wa Aljanu ko aci yankan?
Amsa: Baya halatta musulmi yayi yanka wa aljanu ko yaci yankan da akayi wa Aljanu.
Dalili: An rawaito daga Aliyu bin Abi dalib Allah ya ƙara masa yarda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: Allah ya tsine wa wanda yayi yanka wa wanin Allah. Sahih Muslim: 1978.
Wannan hadisi ya shafi Aljanu da wasunsu, baya halatta Musulmi yayi yanka abisa umarnin aljani.
Read More…