Yadda ake Sallar gawa

Hukuncin Sallar gawa: Sallar gawa Fardu kifaya ce( Idan wasu daga cikin musulmai suka yi ta to ta faɗi akan saura).

Yaya akeyin Sallan gawa?

Kamar ko wacce Sallah ana buƙatar limami wanda zaiyi jagorancin sallar, Idan mamcin na miji ne Limami zai tsaya ta kansa, idan kuma mace ce zai tsaya a tsaƙiyarta, Sannan ba’ayin iƙama, da zarar an haɗu kawai sai liman ya shige yayi kabbara a fara sallah.

Raka’oi nawa ne?

Sallar gawa bata da raka’oi ana yinta ne a tsaye har a kammala, babu ruku’i babu sujudi.

Kabbarori nawa akeyi?

Ana kabbaroi Huɗu ne.

Me ake faɗi bayan ko wani kabbara?

Kabbra ta farko: Za’a karanci Fatiha.

kabbara ta biyu: Za’ayi Salati wa Annabi

kabbara ta uku: Za’ayi addu’a wa mamaci,

kabbara ta huɗu: Za’ayi addu’a wa kayi da mamatan musulmi baki ɗaya

bayan anyi wa’innan kabbarori huɗu sai a sallame. Shikenan An kammala Sallar.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: