Yin Addu’a Da Wani Yare Ba Larabci Ba Acikin Sallah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai Tambaya: Assalamu_Alaikum
Tambayata anan shine. shin mutum zai iya rokon Allah da harshen hausa cikin sujjada yayin sallar farilla?
MISALI azahar, la,asr, ko maghariba.

Amsa a taƙaice:

Babu laifi ga wanda bai iya yaren Larabci ba yayi Addu’a da yaren sa acikin Sallah. Amma ya wajaba a gareshi yayi ƙoƙari wurin koyon Yaren larabci gwargwadon yadda zai sauƙe farillar da take kansa. Kuma abinda yafi dace wa shine yayi ƙoƙari wurin haddace Addu’oin da aka rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam domin ya rinƙa yin su acikin Sallar sa.

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya Allah yayi masa rahama yace:

Ya halatta Mutum yayi Addu’a da larabci ko wani yare da ba larabci ba, domin Allah yasan nufin mai addu’an da buƙatar sa, koda mai addu’ar bai furta abinda ke cikin zuciyarsa ba.Majmu’u Fatawa: 22/488-489

Kamar yadda mukayi bayani a sama Yin Addu’a da wani yare ba larabci ba yana halatta ne kawai ga wanda bai iya yaren larabci ba, amma baya halatta ga wanda ya iya yaren larabci yayi amfani da wani yare wurin roƙon Allah.

Allah shine mafi sani

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories