Allah maɗaukakin sarki yace:
Lalle Sallah tana katange Mutum ga barin aikata Alfasha da Munanan ayyuka
Surat Ankabut: Aya 45
Tambaya anan shine da yawa daga cikin musulmai suna yin Sallah kullun amma kuma zaka gansu suna aikata munanan laifuka, wani lokaci ma da zarar sun kammala Sallar sai kaga sun koma aikinsu mara kyau. Toh ina matsayin wannan ayah da tazo a Al-Qur’ani?
Toh haƙiƙa ya dace musani cewa akwai banbanci tsaƙanin tsaida Sallah da kuma yin Sallah, wanda da yawa daga cikin mutane suna yin Sallah ne ba suna tsaida Sallah ba. Kuma a Al-Qur’ani duk inda Umarni yazo da yin Sallah Allah yana bada Umarni ne a tsaida Sallah ba ayi Sallah ba wanda wuraren suna da yawa duk mai karanta Al-qur’ani yasan da haka ba sai mun kawo su anan ba.
Toh menene tsaida Sallah?
Tsaida Sallah shine mutum ya tsaida ita da gaɓɓansa da kuma zuciyarsa, yayi ta yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar, sannan kuma yayi ta domin Allah, sannan kuma yayi ta zuciyarsa na halarce a lokacin Sallar, ba wai yana Sallah zuciyarsa tana wani wuri ba, ko yana tunanin wani abu ba.
Yayi Sallah ya cika sharruɗanta, da wajibanta, da Sunnoninta, da kuma yanayinta, bawai yayi kawai yadda yaga mutane sunayi ba.
Irin wannan Sallar ne take hana mutum aikata Alfasha da munanan ayyuka, Allah yasa mudace.
Leave a Reply