Hukunci idan Ranar Idi ya hadu da Juma’a

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tambaya: Menene Hukunci idan Juma’a ta haɗu da ranar idi?

Amsa: Maluma sun samu tsaɓani game da wanda yayi Sallar idi shin Wajabcin Juma’a zata faɗi a kansa a bisa zantuka biyu shahararru.

Na farko: Wajabcin Juma’a bata faɗi a kansa ba, Wannan Shine Mazahaba ta Jamhur. Hanafiyya, Shafi’iyya da Malikiyya. Mafi yawancin Malumar Fiqhu suna tafiya kan wannan, kuma shine zaɓi na Ibnul Munzir, da Ibnu Hazm, da Ibnu Abdul Bar.

Dalilan su: Sun kafa Hujja da Alƙur’ani wurin Faɗin Allah acikin Suratul Jumu’a aya ta tara Allah yace:

Yaku wa’inda sukayi Imani, idan akayi kira zuwa Sallah ranar Juma’a ku tafi zuwa ga Ambaton Allah kubar cinikayya.

Suratul Juma’a Aya: 9

Anan sukace Allah yayi umarni ayi Sallar Juma’a kuma bai keɓance ranar idi ba. Saboda Haka ya shafi dukkan ranaku Har da ranar idi.

Dalilin su na biya Athar da aka rawaito daga Abu Ubayd yace:

Sannan nayi Sallar idi tare da Usman bin Affan, kuma wannan ranar ya dace da ranar juma’a, sai yayi sallah kafin yayi huɗuba, sannan sai yayi huɗuba yace: “ya ku mutane, wannan rana ne da idi biyu suka haɗu muku, wanda yake so ya jira Sallar juma’a daga cikin mutanen ƙauye to ya jira, wanda kuma yake son ya koma to na bashi izini

Bukhari: 5571

Sukace dalili acikin wannan athar ɗin shine Usman Bin Affan ya keɓance wa’inda suke wajen gari ne wanda Juma’a bata wajaba akan su ba, amma banda ƴan gari.

Sannan suka sake kafa Hujja da cewa Ai Juma’a Farilla ce, ita kuma idi sunnah ce, kuma Sunnah baya faɗar da Farilla.

Almugni: 2/265

Wannan shine kaɗan daga Hujjojin wa’inda suke ganin wajabcin Sallar Juma’a bata faɗi idan ya haɗu da ranar Idi.

Magana ta biyu itace: duk wanda yaje Sallar Idi ranar da Juma’a ta haɗu da idi to wajabcin Juma’a ta faɗi akan sa, duk da cewa Wajibi ne ga limamin gari yayi sallar, domin wa’inda suke so suyi sallar suyi tare dashi. Wannan itace Mazahaba ta Hanabila(Kasshaful Kanna: 2/40,. Almugni: 2/265)

Kuma wannan shine zaɓin Imam Ibnu Taimiyya, da Ibn Baz da ibnu Uthaimeen. Sannan An rawaito shi daga wasu daga cikin Sahabbai kuma ba’a samu wanda ya tsaɓa musu ba.

Majmu’u Fatawa ibn Taimiyya: 24/211

Ga Dalilan su kaman Haka:

An rawaito daga Iyas ɗan Abi Ramlata yace: naji Abi Sufyan yana tambayar Zaidu bin Arkam yace: shin ka Halarci Idi guda biyu da suka haɗu tare da Manzon Allah? (Ma’ana idi da Juma’a kenan a rana ɗaya) sai yace Eh. Sai yace yaya Annabi yayi? Sai yace: yayi Sallar Idi sannan sai yayi rangwame game da Juma’a, yace: Wanda yaso yayi sallar Juma’a to yayi

Abu Dawud: 1070, Annasa’i: 3/194. Ibnu Maja: 1310

Sannan Sukace: Ranar Juma’a Idi ne, hakanan ranar Sallar Azumi da Sallar layya, Kuma Yana daga cikin Sha’ani na Shari’a idan aka samu ibadoji guda biyu wanda Jinsin su guda suka haɗu sai a shigar da ɗaya ƙarƙashin ɗaya. Kamar yadda alwala yake shiga ƙarƙashin wanka, hakanan kamar yadda idan wanka biyu na wajibi suka haɗu to ɗaya ya shiga ƙarƙashin ɗaya.

A taƙaice: akwai tsaɓani tsaƙanin Maluma kan wannan Mas’ala kamar yadda mukayi bayani, saboda haka duk wanda ya ɗauki dalili da Mazhabar da tafi kwanta masa baiyi laifi ba. Haka nan kuma an tambayi Lajna ta masu Fatawa ta Sa’udiyya game da wannan Mas’ala suka bada fata wa cewa duk wanda yaje sallar idi to wajabcin juma’a ta faɗi a kansa, idan yaga dama yaje idan bai ga dama ba kada yaje, amma zuwansa shi yafi domin yayi sallah tare da Musulmai. Amma zaiyi sallar Azahar.

Sannan Game da Cewa duk wanda yayi sallar Idi to Sallar Juma’a ta faɗi akan sa har da Sallar azahar wannan kuskure ne domin babu wani dalili akan sa kamar yadda maluman suka bayyana.

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories