IDAN IDI YA KASANCE A RANAR JUMA'A TO BABU WAJIBCIN SALLAR JUMA'A A RANAR:

Danna nan domin shiga group na karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo


Idan idi ya kasance a ranar Juma’a to babu wajibcin sallar Juma’a a ranar; wannan hukuncin ne za a iya fahimta in aka yi kyakkyawan nazari cikin hadithai biyar da suka zo cikin wannan babin, hadithan kuwa su ne kamar haka:- (1) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,070 da Imam Ibnu Majah hadithi na 1,326 da isnadi sahihi daga Iyas Dan Abii Ramlah ya ce:-
((شهدت معاوية بن ابي سفيان وهو يسال زيد بن أرقم قال: أشهدت مع رسول الله صلى الله عليه وسلم عيدين اجتمعا في يوم؟ قال: نعم. قال: فكيف صنع؟ قال: صلى العيد ثم رخص في الجمعة، فقال: من شاء ان يصلي، فليصل))
. Ma’ana: ((Na halarci Mu’awiyah Dan Abii Sufyaan yana tambayar Zaid Dan Arqam ya ce: Ko ka halarci Idi biyun da suka hadu a rana guda tare da Manzon Allah? Sai ya ce: Na’am. Sai ya ce: to yaya ya yi? Sai ya ce: Ya yi sallar Idin sannan ya rangwanta yin sallar juma’a, ya ce: Wanda ya so yin sallar sai ya yi sallar)). (2) Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadithi na 1,329 da isnadi sahihi daga Sahabi Abdullahi Dan Umar ya ce:-

((اجتمع عيدان على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم، فصلى بالناس ثم قال: من شاء ان يأتي الجمعة فليأتها، ومن شاء ان يتخلف فليتخلف)).
Ma’ana: ((Idi biyu sun hadu a zamanin Manzon Allha mai tsira da amincin Allah, sai ya yi wa mutane salla sannan ya ce: Wanda ya so tafiya juma’a to sai ya je ta, wanda kuma ya so zaman gida to sai ya zauna)). (3) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,073, da Imam Ibnu Majah ya ruwaito hadith na 1,327 da isnadi sahihi daga Sahaabii Abu Hurairah cewa:-
((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: قد اجتمع في يومكم هذا عيدان، فمن شاء أجزأه من الجمعة، وانا مجمعون)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Hakika Idi biyu sun hadu a wannan rana taku wanda ya ga dama (hakan) ya isan masa yin juma’a, amma lalle mu za mu yi sallar Juma’a)). (4) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,071 da isnadi sahihi daga Ataa Dan Abi Rabah ya ce:-
((صلى بنا ابن الزبير في عيد في يوم جمعة اول النهار، ثم رحنا الى الجمعة فلم يخرج إلينا، فصلينا وحدانا، وكان ابن عباس بالطائف، فلما قدم ذكرنا ذلك له، فقال: أصاب السنة)).
Ma’ana: ((Abdullahi Bin Zubair ya yi mana salla cikin wani idi a ranar juma’a a farkon yini, sannan sai muka tafi juma’a sai kuma (a matsayinsa na liman) bai fito zuwa gare mu ba, (saboda haka) sai muka yi salla kowa shi kadansa. (a lokacin) Ibnu Abbas yana Taa’if to da ya dawo sai muka gaya masa abin da ya faru, sai ya ce: (Abullahi Dan Zubair) ya dace da Sunnah)). (5) Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 1,072 da isnadi sahihi daga Ataa Dan Abii Rabah ya ce;-
((اجتمع يوم جمعة ويوم فطر على عهد ابن الزبير، فقال: عيدان اجتمعا في يوم واحد، فجمعهما جميعا، فصلاهما ركعتين بكرة لم يزد عليهما حتى صلى العصر)).
Ma’ana: ((Ranar juma’a da ranar karamar salla sun hadu a zamanin Ibnu Zubair, sai ya ce: Idi biyu sun hadu a rana guda, sai ya hada su gaba daya ya sallace su raka’a biyu da safe, bai kara wata salla a kan su ba har ya yi sallan La’asar)). In aka kyautata nazari cikin wadannan hadithai za a fahimci cewa a duk ranar da Idi ya kasance ranar Juma’a, to sallar Juma’ar wannan rana ba ta zamantowa wajiba a kan al’ummar Musulmi. Wannan shi ne abin da ya bayyana a garemu, muna kuma sane da tattaunawar da Malamai suka yi game da mas’alar. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories