ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA, BA WAI HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR YADDA MASU BIDI'A KE CEWA BA(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN
DA ALLAH YA HALITTA,
BA WAI HASKEN MANZON
ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR
YADDA MASU BIDI’A KE CEWA
BA:
Sau da dama ‘Yan’uwa Musulmi za
ku rika ganin cewa Sufaye da
dukkan wadanda suka saki hanyar
Shari’ah cikin tafiyar da addininsu
suna barin yin aiki da nassin
Alkur’ani, ko nassin ingantaccen
hadithi, su koma suna yin aiki da
nassoshin da ko dai su ne suka
kirkiro su da kansu, ko kuwa a’a
wasu hadithai ne masu rauni
matuka, ko kuwa wasu hadithai ne
na karya a bisa ittifakin masana
ilmin hadithi!!
Misali: Imam Abu Daawuud ya
ruwaito hadithi na 4,702, da
Imamut Tirmizi hadithi na 2,155, da
Imam Ahmad hadithi na 22,757
daga Sahabi Ubaadatu Dan
Saamit, haka nan ma Imamul
Haakim cikin Mustadrak dinsa
hadithi na 3,693, da Imamut
Tabaraanii cikin Almu’ujamul
Kabeer hadithi na 12,060, da
Imamul Baihaqii cikin As-Sunanul
Kubraa hadithi na 18,157 daga
Sahaabi Abdullahi Dan Abbas,
sannan Imamul Albaanii da sauran
masana Ilmin Hadithi sun inganta
shi, dukkan wadannan Sahabbai
biyu ko wannensu ya ce:-
(( ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ:
ﺍﻥ ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﻠﻢ، ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ: ﺍﻛﺘﺐ. ﻗﺎﻝ: ﺭﺏ
ﻭﻣﺎﺫﺍ ﺍﻛﺘﺐ؟ ﻗﺎﻝ: ﺍﻛﺘﺐ ﻣﻘﺎﺩﻳﺮ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﺣﺘﻰ
ﺗﻘﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Na ji Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah yana cewa:
Lalle farkon abin da Allah Ya
halitta shi ne Alkalami, sannan Ya
ce da shi: Ka rubuta, to sai ya ce:
Ya Ubangijina mene ne zan
rubuta? Sai Ya ce: Ka rubuta
kaddarorin kome har Sa’ah ta
tsaya)). Intaha.
Kamar yadda kuke gani wannan
nassi ne na sahihin hadithi, to
amma kuma duk da haka sai ga
shi Aluusii ya hikaito daga Sufaye
cikin tafsirinsa mai suna Ruuhul
Ma’aanii 17/105 cewa sun ce ya zo
cikin Hadithi cewa Annabi mai tsira
da amincin Allah ya ce wa Sahabi
Jabir Dan Abdullahi :-
(( ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ.((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da
Allah Madaukakin Sarki Ya halitta
shi ne hasken Annabinka)). Intaha.
Don Allah ku duba ku ga irin yadda
Sufaye suka bar yin aiki da
ingantaccen hadithi, suka koma
suka kirkiro wani hadithin karya
suka jingina shi zuwa ga Annabi
mai tsira da amincin Allah, ta inda
kuwa za ku fahimci cewa hadithi ne
karya shi ne: Sam ba ya rubuce
cikin littattafan hadithi sanannu,
wannan shi ya sa ma a lokacin da
Sheik Muhammad Jameel Zainu
yake bayanin hadithai na karya
cikin littafinsa Mai suna: Minhaajul
Firqatin Naajiyah Wat Taa’ifatil
Mansuurah shafi na 74 ya ce:-
(( ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ.” ﻣﻮﺿﻮﻉ((
. ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da
Allah Ya halitta shi ne hasken
Annabinka”. maudhuu’ine)). Intaha.
Haka ma Sheik Albanii ma a cikin
littafinsa Silsilatul Ahaadithis
Sahiihah 1/457 a lokacin da ya
kawo hadithin nan na 2,996 da
Imam Muslim ya ruwaito cikin
Sahihinsa watau:-
(( ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ ﻭﺧﻠﻖ ﺍﻟﺠﺎﻥ ﻣﻦ ﻣﺎﺭﺝ
ﻣﻦ ﻧﺎﺭ، ﻭﺧﻠﻖ ﺍﺩﻡ ﻣﻤﺎ ﻭﺻﻒ ﻟﻜﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’an: ((An halicci Mala’iku daga
wani irin haske ne, sannan an
halicci Aljannu daga wani irin
harshen wuta mai launin baki-baki
ne, sannan kuma an halicci Adamu
ne daga abin da aka siffanta muku)
). Sai shi Albaanii ya ce:-
(( ﻓﻴﻪ ﺇﺷﺎﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺑﻄﻼﻥ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻤﺸﻬﻮﺭ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺎﺱ” :ﺍﻭﻝ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻧﺒﻴﻚ ﻳﺎ ﺟﺎﺑﺮ ”
ﻭ ﻧﺤﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﻘﻮﻝ ﺑﺎﻧﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺧﻠﻖ ﻣﻦ ﻧﻮﺭ، ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺩﻟﻴﻞ
ﻭﺍﺿﺢ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻓﻘﻂ ﻫﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺧﻠﻘﻮﺍ ﻣﻦ
ﻧﻮﺭ، ﺩﻭﻥ ﺍﺩﻡ ﻭﺑﻨﻴﻪ، ﻓﺘﻨﺒﻪ ﻭﻻ ﺗﻜﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﺎﻓﻠﻴﻦ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Cikin wannan hadithin
akwai isharar cewa hadithin nan da
ya shahara cikin harsunan mutane,
watau: “Ya Jabir farkon abin da
Allah Ya halitta shi ne hasken
annabinka” da ma irinsa daga cikin
hadithan da suke cewa: Annabi
mai tsira da amincin Allah an
halicce shi ne daga wani irin haske
magana ce ta karya. Lalle wannan
hadithin hujja ce karara da ke
nuna cewa: lalle Mala’iku ne kadai
aka halitta su daga wani irin haske,
amma banda Adamu da ‘ya’yan
shi. Sai ka fadaka, kada ka
kasance daga cikin gafalallu)).
Intaha.
Allah Ya shiryar da sufayenmu
cikin wannan Al’ummah, da ma
dukkan sauran karkatattu da ake
da su cikin wannan Al’ummah
Muhammadiyyah.
Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya
gaskiya ce Ka ba mu ikon bin ta,
Ka nuna mana karya karya ce Ka
ba mu ikon guje mata. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

7 responses to “ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA, BA WAI HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR YADDA MASU BIDI'A KE CEWA BA(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
 1. Adam abualamin Avatar
  Adam abualamin

  Allah yakara mana son gaskiya da aiki dashi.

 2. Nazifi rabiu Avatar
  Nazifi rabiu

  Allah ya saka da Alkhairi malam.

 3. Rabiu Rilwanu Avatar
  Rabiu Rilwanu

  Allah yasaka maka da alkhairinsa’yashiryar damu hanya madaidai ciya.

 4. Rabiu Rilwanu Avatar
  Rabiu Rilwanu

  ya Allah kashir yaddamu.

 5. Kameel agadasawa Avatar

  Allah yatsinewa makiya shugaba duk wata daraja ta shugaba sai sunyi kokarin disasheta allah yarabamu daku.

 6. Ibrahim Halliru Avatar
  Ibrahim Halliru

  ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA, BA WAI HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA?
  Wato abin da yawancin mutane basu gane ba shine, a har kullum shi Musulunci yana a yanda yake ba ya canzawa. Amma su Musulmai, abu ne mai sauƙi ainun su iya canza fahimtarsu da addininsu. Sai dai kuma akwai matuƙar wuyar gaske ainun su iya tursasa gamaiyar gurɓatacciyar fahimta da shi addinin.
  Dangane da wannan batu, shin kana tunanin cewa halitta na farawa ne yayin shigar ciki (juna biyu)? Domin idan hakane to lallai bai kamata ba Allah Ya yika takarkari kace sai ka nannagi na amale, tabbas, za kai ƙasa a gwiwa.
  Bari in bada wata Ƴar satar amsa. Amma da fari, zan faiyace ainihin batun da ya kawo taƙaddamar, wato, FARA.
  Duk inda ka ji ko ka ga wannan kalma, lallai magana ake da ta shafi LOKACI. To kwa indai har maganar lokaci ake ba a buƙatar gardama kan me aka fara ko me ya biyo baya. Dalili kuwa shine shi kanshi lokacin bai samu ba sai yayin halittar ita duniyar da muke ciki. Kenan daga ɗaukacin duniyoyin da Allah ya halitta, ba lallai ne ba dukkansu su zama suna aiki da lokaci – Allah shine masani. Amma dai sanannen abu gare mu shine “Big Bang Theory” – wata fahimta da Allah ya sanar ga masu ilmin kimiyya, ta tabbatar da cewa kafin wanna Babbar Tsawa lallai babu lokaci, sarari ko wani abin da za a iya kira da ƙwayar zarra. Shi ya sanya ma waɗanda suke faɗin wai Allah yana sama, haƙiƙa sune ke dakon gawurtaccen jahilci. Domin saman da suke nunawa, ta samu ne bayan faruwar Babbar Tsawar.
  Al’amarin halittar ruhin ɗan adam kuwa, lamari ne da ya tsallake wannan duniyar, ya shiga wata duniyar marar aiki da lokaci na ita wannan duniyar da muke ciki – ko kuwa ma baki ɗaya.
  Da wannan nike baiwa masu inkarin kasancewar Annabi Muhammadu (SAW) farkon halitta da sui hakuri, su sallama duk abin da Allah bai basu fahimtarsa ba. Ni kaina fahimta ta bata kai ga wannan ba, amma dai na ji ana faɗi. Kuma waɗanda ke faɗin haƙiƙa ma’abota ilmi ne, gaya. Don kana iya kammala buge-bugen ka da binkice-binkicenka, ka dawo ba tare da wani abu ba fiye da wadda suka gaya maka dun da fari.
  Ai hattara!

 7. Abdullahi sokoto Avatar
  Abdullahi sokoto

  Don Allah ka yimaka bayani gama hasken manzon Allah

Leave a Reply

Categories
Latest updates